"Na Yanke Wa Saurayina Gaba Ne Saboda Ya Ki Aurena Kuma Zai Auri Wata"

A ranar Litinin ne jami'in hulɗa da jama'a Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana yadda suka cika hannu da wata matashiyar budurwa 'yar shekara 25, wadda ake zargi da yanke wa saurayinta gaba saboda zargin ya yaudareta.

Bayan da suka samu nasarar kamata, jami'in ya saki fitar da suka yi da matashiyar inda ya bayyana cewa:

Sunana Maimunatu Idris haifaffiyar garin Maigatari ta jihar Jigawa da ke maƙwabtaka da Kano. Na zo Kano ne buki, inda muka haɗu da shi a wani keɓaɓɓen wuri. Muna tsaka da fira sai ya ce min kanshi yana ciwo, don haka sai na ce masa ya tashi mu fita mu samo magani, haka kuwa aka yi, muka fita muka sawo magani muka dawo. 

Tun da muka dawo yake sharar barci, na yi, na yi ya tashi amma hakan ya faskara, hakan ya sa sai na ɗauki wayarsa na fara dubawa, can sai na saurari wata tattaunawa da suka yi a kaina ta audio, Wanda maganganun da na ji ne suka ƙara dugunzuma har suka sa na yanke masa gaba, kuma na ɗauke shi na shigar da shi bayin ɗakin da muke na yi masa wanka saboda jinin da ya ɓata shi.

Na yi masa wannan aikin ne, a ranar Lahadi da misalin 11:00 na safe, saboda ya ce zai yi aure, kuma ba ni zai aura ba. Wanda ya san mun kwashe tsawon shekaru 6 muna soyayya har ta kai ga an sa mana rana da shi, daga baya aka warware. Bayan na samu wani, shi ma an sa min rana da shi, amma sai ya kada baki ya ce lallai ba zan aure shi ba. Haka nan soyayya ta kwashe ni, na biye masa na rabu da wancan. Amma kwatsam sai ya zo min da labarin zai yi aure, sai kuma ga wannan firar da na ji sun yi a kaina a WhatsApp nashi. Wanda hakan ya sa na rasa kaina, na rasa me ma zan yi. Sai na tuna da ma na taho da wuƙa tun daga gida Maigatari, kawai sai na yi amfani da ita na yanke masa gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post