"Idan Muka Maka Rarara a Kotu Wallahi Sai Mun Yi Winning" In Ji Wasu Daga Cikin Kungiyar 13-13

A wata fira da ɗaya daga cikin mawaƙan Hausa na zamani Alhaji Ali Jita kuma ɗan masana'antar Kannywood ya yi da abokin aikinsa Adam A. Zango jarumi, mawaƙi kuma makiɗi na masana'antar ta Kannywood, a tashar Zauren Jita wadda ake kira da Jita Talkshow 

Jarumin ya bayyana dogon labarin abin alhinin da ya faru da shi kafin ya tsunduma harkar fina-finai, Zango ya bayyana yadda Allah ya ceci rayuwarsa da ta wata tsohuwa mariƙiyarsa daga hannun arnan Zangon Kataf a yayin da aka yi faɗan ƙabilu a wancan lokacin.

Sai dai da alama, a firar ba wannan ne batun da ya fi jan hankalin masu sauraro ba. Abin da ya fi ɗaukar hankalin masu sauraro shi ne yadda furodusan, Adam A Zango ya bayyana yadda tafiyarsa da Rarara ta zama asarar lokaci a lokutan da suka gabata, kasancewar ya bayyana cewa: "Ina ajiye aikin da zan samu naira miliyan ɗaya domin in bi Rarara mu yi tafiya, ƙarshe mu dawo ya ba ni naira dubu ɗari uku (₦300,000), sannan ya ce min za mu yi magana, amma dai har yanzu ba mu yi wata magana ba, iya sallamar ke nan. Ina jin za mu yi tafiya kusan goma sha wani abu da shi, amma bai taɓa ba ni sama da ₦300,000.

A cikin tattaunawar ya taɓo batun tafiyarsu ta ƙungiyar 13-13 wadda a cikin tafiyar har da shi mai gabatar da shirin wato Ali Jita, inda ya bayyana cewa: "Da za mu yi amfani da takardar yarjejeniyar da aka ƙalla a ƙungiyar 13-13 mu maka Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (RARARA) kotu, to wallahi da sai mun yi winning. Sai dai ba mu yi hakan ba."

A firar Adam A Zango ya bayyana ƙarara cewa shi ba shi da wata tsayayyar jam'iyya, shi mutum zai zaɓa ba jam'iyya ba. Don haka a yanzu ba shi tallar kowa, duk da dai kuma duk wanda ya ba shi kuɗi zai amsa, amma ba zai ƙara bin tafiyar wani ƙato ba.

A fitar mun jiyo inda Ali Jita da Zango suke raha kan wani batu da mawaƙi Nura M. Inuwa yake yi a a lokacin tafiyarsu ta 13-13, wanda Ali Jita ya yi alƙawarin gayyatar M.Inuwa domin ya yi sharhin maganar da yake yi, idan za a ɗauke su hoto a cikin jama'a na cewa "KA HALAKA."

Post a Comment

Previous Post Next Post