Hukumar Jin Daɗin Alhazan ta Jihar Jigawa ta buɗe rajistar aikin Hajjin shekarar 2027, tare da kayyade Naira miliyan 7.5 a matsayin zubin farko na kuɗin aikin Hajji da maniyyata za su biya.
Hukumar ta kuma sanar da cewa saura kwanaki 87 kacal a rufe rajistar, inda ta buƙaci masu niyyar zuwa aikin Hajji su gaggauta yin rajista.
Darakta Janar na Hukumar, Ahmed Labbo, ne ya bayyana hakan a yayin wata ganawa da jami'an hukumar na shiyyoyi 27 na ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Dutse.
Labbo ya ce fara karɓar kuɗin tun da wuri zai bai wa maniyyata damar tabbatar da gurabensu, tare da kauce wa cunkoso da ake samu a ƙarshen lokaci.
Ya bayyana cewa wannan matakin ya yi daidai da umarnin Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) da kuma hukumomin Saudiyya, waɗanda suka buƙaci a fara shirye-shiryen aikin Hajji tun da wuri.
A cewarsa, hukumomin Hajji da Umrah na Saudiyya sun sanya watan Satumba a matsayin wa'adin ƙarshe na rajistar maniyyata daga sassa daban-daban na duniya.
Saboda haka, ya umarci jami'an hukumar na shiyyoyi da su ƙara wayar da kan al'umma tare da tabbatar da cewa an cike dukkan guraben da aka ware wa jihar kafin cikar wa'adin.
Darakta Janar ɗin ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa ci gaba da bai wa hukumar cikakken goyon baya, yana mai cewa hakan ya taimaka wajen gudanar da ayyukan Hajji cikin nasara a jihar.
