Jami'an Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (DSS) sun kama 'yar jarida Zainab Sodiq, wadda ke bibiyar ayyukan ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore. A halin yanzu ana tsare da ita a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Rahotanni sun ce kama Zainab ya haifar da damuwa a tsakanin 'yan jarida, ƙungiyoyin fararen hula da magoya bayanta, inda da dama ke kira da a sake ta cikin gaggawa. Lamarin ya kuma sake tayar da muhawara kan 'yancin aikin jarida a Najeriya.
Har zuwa yanzu, ba a bayyana takamaiman dalilin da ya sa aka kama ta ba, kuma DSS ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke bayyana musabbabin tsare ta ba.