Manyan ƙwararrun likitoci sun gargaɗi 'yan Najeriya da su guji yin wanka da ruwan sama da ba a tsarkake ba, suna mai cewa hakan na iya haddasa cututtukan fata irin su ƙurajen fungi (ringworm), cutar ƙafar fungi (athlete's foot), marurai, da kuma cutar fungi a yankin mara (jock itch).
Masanan sun bayyana cewa ruwan sama ba ya kasancewa mai tsabta gaba ɗaya, domin yayin da yake saukowa daga sararin samaniya yana iya haɗuwa da ƙura, ƙwayoyin cuta, fungi, kashin tsuntsaye, sinadarai masu gurbata muhalli da sauran datti. Haka kuma, idan aka tara shi a cikin tankuna ko kwantena marasa tsafta, haɗarin gurɓacewarsa na ƙaruwa.
Sun ce yawan amfani da irin wannan ruwa wajen yin wanka, musamman ga masu rauni ko fata mai laushi, na iya janyo kamuwa da cututtukan fungi da ƙwayoyin cuta, tare da haddasa kaikayi, ja, da kumburin fata.
Farfesa a fannin Magunguna da Cututtukan Fata, Madubuko Roli, ta bayyana cewa ruwan sama na iya ɗaukar sinadarai masu cutarwa, ƙwayoyin cuta da ƙwayoyin fungi yayin da yake saukowa ko kuma idan ya gangaro daga rufin gidaje.
Ta ce hakan na iya haddasa cututtukan fata kamar ringworm, athlete's foot, jock itch, kumburin gashin fata (folliculitis), da kuma yawaitar marurai.
Roli, wadda ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Benin, ta shawarci jama'a da su rika tace ko tsarkake ruwan sama kafin amfani da shi, tare da kula da tsaftar tankuna da wuraren adana ruwan.
A nasa ɓangaren, ƙwararren masanin guba da lafiyar muhalli, Onaeko Oluwawemimo, ya ce ruwan sama, musamman wanda ya gangaro daga rufin gidaje, na iya ƙunsar sinadarai masu haɗari kamar ƙarafa masu nauyi da magungunan kashe kwari.
Ya ƙara da cewa idan ruwan ya ƙunshi ƙwayoyin cuta, fungi ko ƙwayoyin virus, yana iya haifar da cututtukan numfashi kamar mashako da ciwon huhu, baya ga matsalolin fata.
Oluwawemimo ya ba da shawarar cewa kafin amfani da ruwan sama, ya kamata a tafasa shi, a tace shi, ko a yi amfani da sinadarin chlorine ko na'urorin kashe ƙwayoyin cuta ta hasken UV domin tabbatar da amincinsa.
Masanan sun jaddada cewa bin waɗannan matakan kariya zai taimaka wajen rage haɗarin kamuwa da cututtuka, musamman a lokacin damina da ake yawan amfani da ruwan sama a gidaje.