Malama Ta Mika Kanta Ga ’Yan Sanda Bayan Zargin Dukan Dalibi Har Ya Mutu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta bayyana cewa babbar wadda ake zargi da hannu a mutuwar wani ɗalibi mai shekaru 12, Misis Dim Ebere, mai shekaru 47 kuma malama ce a wata makaranta da ke Adazi-Enu, ta miƙa kanta ga ofishin ’yan sanda na Neni da ke ƙaramar hukumar Anaocha.

A baya dai rundunar ta ƙaddamar da farautar wadda ake zargin bayan rahotanni sun nuna cewa yaron ya rasu sakamakon raunukan da ake zargin ya samu ne bayan da malamar ta yi masa bulala a makaranta.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Tochukwu Ikenga, ya fitar a ranar Asabar, ya ce wadda ake zargin ta miƙa kanta ne bayan dogon aikin nema da Rundunar Kare Makarantu ta Anambra (Safe School Protection Squad) ta gudanar tare da haɗin gwiwar jami’an ofishin ’yan sanda na Neni.

Ikenga ya ce an kuma samu nasarar ne ta hanyar ci gaba da tattaunawa da haɗin gwiwa da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki a garin Adazi-Ani.

Ya bayyana cewa a halin yanzu wadda ake zargin tana tsare a hannun ’yan sanda, kuma za a miƙa ta zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (State Criminal Investigation Department – SCID) da ke Awka domin kammala binciken da ake yi.

Sanarwar ta ce:

“Bayan ci gaba da gudanar da aikin neman wadda ake zargi da Rundunar Kare Makarantu ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra ta yi tare da jami’an ofishin ’yan sanda na Neni, da kuma ci gaba da tattaunawa da shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki a Adazi-Ani, babbar wadda ake zargi, Misis Dim Ebere mai shekaru 47, ta miƙa kanta ga ofishin ’yan sanda na Neni.

“A halin yanzu tana tsare a hannun ’yan sanda, kuma za a tura ta zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar da ke Awka domin kammala binciken.

“Rundunar tana yabawa al’ummar Adazi-Ani, masarautar gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa haɗin kan da suka bayar, wanda ya taimaka wajen miƙa kan wadda ake zargin.

“Muna tabbatar wa iyalan mamacin da daukacin jama’a cewa rundunar za ta tabbatar an yi adalci a wannan lamari.

“Har ila yau, rundunar tana kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji ɗaukar doka a hannunsu, sannan su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen ci gaba da bincike da sauran ayyukan tabbatar da tsaro a faɗin jihar.”

Post a Comment

Previous Post Next Post