Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wata tsohuwa ‘yar Najeriya mazauniyar Birtaniya mai shekara 67, Mary Yetunde Barek, bayan an gano kilo 13 na hodar iblis da aka ɓoye cikin bawon ayaba a cikin kayanta a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama matar ne yayin da take shirin hawa jirgin Virgin Atlantic zuwa birnin London, inda ta amsa cewa hodar iblisin mallakinta ce.
Hakazalika, hukumar ta kama wani ɗalibin digirin digirgir a Jami'ar Putra ta ƙasar Malaysia, Nwabueze Felix Onyeka, a Jihar Anambra, bayan gano kilo 5.8 na hodar iblis da aka ɓoye cikin kwalayen abin sha na Orijin Bitters da ake shirin kaiwa Malaysia.
A wasu samamen daban, NDLEA ta kuma kama mutane da dama a jihohin Taraba, Kaduna, Ebonyi, Filato da Gombe tare da ƙwace tramadol, methamphetamine da tabar wiwi masu yawa.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami'an hukumar kan nasarorin da suka samu, tare da umartar su da su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar.
