Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta Najeriya (NiHSA) ta yi gargaɗin cewa ambaliyar ruwa da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar na iya ci gaba har zuwa watan Satumba.
Darakta Janar na hukumar, Umar Mohammed, ya bayyana cewa hasashen ambaliyar ya samo asali ne daga bayanan da NiHSA ta tattara, yana mai gargadin cewa lamarin na iya ƙara muni tsakanin watan Agusta da Satumba idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba.
Da yake jawabi ta bakin shugaban Sashen Tsarin Bayanai na Ƙasa (GIS) da Fasahar Nesa (Remote Sensing) na NiHSA, Emmanuel Tuna, Mohammed ya ce hukumar ta riga ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliyar tun kafin ta fara faruwa.
Ya ce, "Mun hango wannan tun da wuri. Mun san zai faru."
Ya ƙara da cewa, "Ambaliyar da ake gani a yanzu ita ce farkon damina. Idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba, cikin watanni 12 na lokacin damina daga Yuli zuwa Satumba, lamarin na iya zama mafi muni fiye da yadda yake a yanzu."
Mohammed ya ce ana sa ran ambaliyar za ta fi tsananta musamman a tsakanin watan Agusta da Satumba.
Baya ga barnar da ambaliyar ke haddasawa ga gidaje da ababen more rayuwa, ya ce NiHSA na matuƙar damuwa da tasirin da hakan zai yi ga hanyoyin samar da ruwan sha, wanda ka iya jefa lafiyar al'umma cikin haɗari.