Pakistan ta bayyana cewa dakarunta sun kakkabo jiragen sama marasa matuƙa guda huɗu da aka ce an harba daga Afghanistan zuwa cikin sararin samaniyarta.
Jami'an tsaron Pakistan sun ce tsarin kariyar sararin samaniyarsu ya gano jiragen marasa matuƙin tun kafin su kai ga wuraren da ake zargi za su nufa, sannan aka yi nasarar kakkabe su ba tare da sun haddasa wata babbar ɓarna ba.
Hukumomi sun ce ana ci gaba da bincike domin gano inda aka harba jiragen da kuma waɗanda ke da hannu a lamarin, yayin da aka ƙara matakan tsaro a kan iyakar ƙasashen biyu.
Har zuwa yanzu, hukumomin Afghanistan ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan zargin da Pakistan ta yi ba.
Lamarin ya sake ƙara nuna damuwar da ake da ita kan tsaro a iyakar Pakistan da Afghanistan, inda ake yawan samun rikice-rikice da hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.