Peter Obi Ya Sha Alwashin Hade Kan Yan Nijeriya

Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, zai dakile saba ka'ida a tafiyar da gwamnati tare da inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Peter Obi

Obi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce shirinsa zai mayar da hankali kan haɗin kan ƙasa, zaman lafiya, adalci da ci gaba mai ɗorewa.

Ya ce gwamnatinsa za ta bai wa ɓangarorin ilimi da lafiya muhimmanci, tare da kafa kwamitin musamman domin rage yawan yara marasa zuwa makaranta. Haka kuma, ya yi alƙawarin bunƙasa ilimin sana'o'i da fasaha (TVET) domin samar da ƙwararrun ma'aikata da ƙarfafa masana'antu.

Obi ya ƙara da cewa za a samar da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin addini wajen inganta cibiyoyin koyar da sana'o'i, tare da ƙarfafa tarbiyya da ilimin zama ɗan ƙasa domin gina amana, shugabanci nagari da haɗin kan al'umma.

Post a Comment

Previous Post Next Post