Raddin Sheikh Shafee'u Yusuf akan Batun Auren Mutu'a ga Prof Makari Sa Sheikh Ibrahim Daurawa
Malamin yana goyon bayan maganar Farfesa Ibrahim Ahmad Makari inda ya ce: "Mas’alar da prof yayi magana haka take balma shine ijma’in malamai cewa aurene ingattace kamar yadda zan kawo nan gaba insha'Allah‚ masu tuhumarsa kan wannan mas’alar guri ɗaya ne kawai za su iya samun abin cewa watau prof cikin maganarsa ya ambace shi da “An-nikãhul- mu’aƙƙat”!‚ Anan ne kawai za su samu abin tuhuma saboda a “isɗilãhin”! malaman “fiƙh”! sunan mas’alar “An-nikãhu bi niyyatuɗ ɗalaƙ”! galiban shine ta'arifin mas’alar a wajen fuƙha’u domin lafazin “An-nikãhul- mu’aƙƙat”! da ta'arifinsa ɗaya yake da nikãhul mut’ati (auren mut’a) da kuma “An-nikãhu ilã ajali”! shiyasa Alhãfiz Ibnu Abdulbarri ya basu ma'ana ɗaya yace:-
وهو أن يتزوج الرجل المرأة بشئ مسمى إلى أجل معلوم يوما أو شهرا أو مدة من الزمان المعلومات على أن الزوجية تنقضي بانقضاء الأجل
(An-nikãhul mu’aƙƙat, An-nikãhu ilã ajali, nikãhul mut’ati) Shine mutum ya auri mace akan sadaƙi ambatacce zuwa wani lokaci sananniyar rana, wata, ko wani tsawon zamani sananne cewa igiyar aurensu tana ƙarewane da ƙarewar wannan lokacin (wannan auren haramun ne)
Alkãfi 1/173
shi yasa ta hanyar bayaninsa na fahimci kalar auren da yake nufi, Anan‚ idan kun fahimce ni prof yana nufin “An-nikãhu bi niyyatuɗ ɗalaƙ”! ne wajen bayaninsa ba kamar yadda ya kira shi da “An-nikãhul mu’aƙƙat”! ba, shi wannan auren da prof yake nufi shine ka auri mace ba tare da sanya sharaɗin rabuwa ba lokacin ɗaurin auren, kaine zaka ƙudurci niyyar zaka saketa nan gaba aranka cewa matuƙar ka aureta zaka riƙeta ne zuwa ɗan wani lokaci ka sake ta‚ shiyasa aka saka masa suna da “An-nikãhu bi niyyatuɗ ɗalaƙ”! ma'ana yin aure da niyyar saki‚ jumhur ɗin malamai sun tafi akan ingancin auren, dalili shine shi mijin daya ɓoye wannan niyyar acikin zuciyarsa hakan bai shafi asalin igiyar aurensu ba‚ ita kuma niyya abune daya shafi zuciya Allah baya kama mutum da'ita harsai ya furta kamar yadda Annabi (SalLalLahu Alayhi WasalLam) ya faɗa
إن الله تجاوز لأمتي عما حدثت به أنفسها مالم يتكلموا أو يعملوا به
Allah ya yafewa Al'ummata, bisa abinda ta zantar a zuciyarta, matuƙar batayi magana ko aiki da shi ba.
Saheeh Bukharee: 1/90, Saheeh Muslim:201, 202.
Dukkan mazãhib guda 4 da muke da su sun halasta wannan auren matuƙar ba'a sanya sharaɗi yayin ɗaura auren ba, Cikin gida mazhabarmu ta malikiyya Imamu Muhammad dirdir cikin littafinsa sharhul kabeer yana faɗa cewa
ولا يضر قصد الطلاق بعد مدة إذا لم يشترطه في العقد.
Kuma niyyar sakin matar bayan wani lokaci ba ta cutar da ingancin auren, matuƙar bai sharɗanta hakan a yayin ɗaura auren ba."
Sharhul-kabeer:238
Idan muka leƙa mazhabin Imam abu Hanifah babban malaminsu mai suna Ibnu Ãbidin yana cewa:
لو تزوجها وفي نيته أن يقيم معها مدة ثم يطلقها، فالنكاح صحيح؛ لأن التوقيت لم يقع في العقد، وإنما هو نية."
Da’ace mutum zai auri mace‚ alhali yana da niyyar zai zauna da ita na wani lokaci sannan ya sake ta to wannan aure ingantacce ne, saboda sanya wa'adin lokaci bai kasance cikin sharaɗin ɗaurin auren ba, illa dai niyya ce kawai (a zuciya).
Al-muhtãr: 3/54
Haka nan idan ka koma mazhabar Imamus shãfi'i za ka ga babban malaminsu Imamun nawawee yana cewa:-
"لو نكحها مطلقًا ونوى أن يطلقها بعد مدة، صح النكاح؛ لأن النية لا تؤثر في صحة العقد."
Da mutum ya auri mace ba tare da sanya wani sharaɗin lokaci ba, amma ya yi niyyar zai sake ta bayan wani lokaci, to auren ingantacce ne; saboda niyya ba ta da tasiri wajen ingancin ɗaurin aure.n"
Raudhatuɗ ɗãlibina:7/42
Hakanan mazhabar Imam Ahmad bin hambal idan ka koma can shima zaka ga malaminsu Ibnu ƙudãma Al-hambali yana cewa:-
"إن تزوجها بغير شرط، إلا أن في نفسه أن يطلقها بعد شهر، أو إذا قضى حاجته منها، فالنكاح صحيح في قول عامة أهل العلم."
Idan mutum ya auri mace ba tare da wani sharaɗi ba, sai dai a zuciyarsa yana da niyyar zai sake ta bayan wata ɗaya, ko kuma bayan ya biya buƙatarsa da ita, to auren ingantacce ne a wurin mafi yawan malamai."
Al-mugni:7/53
Abinda yasa auren ya inganta saboda shi kaɗai ya ƙuduri niyya a ransa bai shafi ingancin auren ba ko kaɗan (saɓanin nikãhut tahlil) domin sanya sharaɗi loƙacin ɗaura auren shine bai inganta ba‚ niyyar da yayi na sakinta wannan shi da IAllah amma ko kaɗan bai shafi asalin ƙulla auren ba.
إنما الأعمال بالنية وإنما لكل امرء ما نوى
Lallai kowanne aiki yana tare da niyya kuma kowanne mutum da abinda yayi niyya.
Sahihul Bukhari: 6953, Saheeh Muslim: 1907"
Bayan malamin ya gama kawo hujjoji daga magabata waɗanda suke ƙara tabbatar da ingancin auren "An-nikãhu bi niyyatuɗ ɗalaƙ", wanda ya nuna Prof ya kuskure da kiransa da suna nikahil mu'aƙƙat. Malamin ya kuma waiwaya kan tsohon rubutun da Malam Aminu Daurawa ya yi tun a shekarar 2021, kan batun auren mutu'a inda ya ce:
"Shi kuma Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa mas’alar auren mut’a da yayi magana akan halascinsa harya jingina maganar ga Abdullahi ɗan Abbas da yace harya mutu yana bada fatwa akan haka‚ maganarsa akwai banbanci tsakanin fatwarsa data prof Sannan kuma Abdullahi ɗan Abbas (RTA) kafin ya rasu ya janye wannan fatwar tasa kamar yadda Imam abu isa Ibnu sarwata Attirmidhy ya ruwaito."