Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Dangote da dillalan mai yayin da farashin fetur ke ci gaba da zama sama da Naira 1,000.
Farashin fetur a Najeriya na iya ci gaba da kasancewa sama da Naira 1,000 kan kowace lita na wani lokaci idan har dillalan mai su ka fara yaƙin rage farashi da matatar Dangote, kamar yadda jaridar The PUNCH ta ruwaito.
Bayan da farashin ɗanyen mai ya faɗi zuwa kusan dala 70 kan ganga a kasuwar duniya.sakamakon sake buɗe hanyoyin jigilar mai ta mashigin Strait of Hormuz, 'yan Najeriya da dama sun yi tsammanin farashin fetur zai ragu.
Amma hakan bai faru ba, domin matatar Dangote ta rage farashi kaɗan ne kawai.
Tun daga ƙarshen shekarar 2024, matatar Dangote ce ke jagorantar ƙayyade farashin fetur a Najeriya, bayan da NNPC ya daina zama babban mai shigo da fetur saboda fara aikin matatar Dangote.
Yayin da ake kira da a rage farashin fetur saboda raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, wani babban jami'in Kamfanin Dangote ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta tambayi masu shigo da mai da ta ba lasisi su rage nasu farashin.
Jami'in, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya ce ya yi mamakin yadda masu shigo da fetur daga Rasha, wanda ya ce ya fi arha, ba su rage farashin sayarwa ba.
