Tarayyar Turai (EU) ta zargi kamfanin Meta Platforms, mamallakin Facebook da Instagram, da karya dokokin Digital Services Act (DSA) saboda amfani da wasu siffofi da hukumomin ƙungiyar suka ce an tsara su ne domin su sa masu amfani dasu su riƙa ɗaukar lokaci mai tsawo a kan manhajojin.
Hukumar Tarayyar Turai ta bayyana cewa siffofi irin su ci gaba da gungurawa ba tare da ƙarewa ba (infinite scrolling), kunna bidiyo kai tsaye (autoplay), saƙonnin tunatarwa (push notifications), da kuma tsarin ba da shawarwarin abubuwan da mai amfani zai kalla bisa halayensa, na iya sa mutane, musamman yara da matasa, su kamu da amfani da shafukan sada zumunta fiye da kima.
A cewar masu sa ido na EU, Meta ba ta yi isasshen bincike ba kan haɗarin da waɗannan siffofi ke haifarwa ga lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwar masu amfani. Haka kuma, sun ce matakan kariyar da kamfanin ya samar, kamar ikon iyaye da kayan sarrafa lokacin amfani da manhajojin, ba su da sauƙin amfani kuma ba su isa su kare yara yadda ya kamata ba.
Hukumar ta buƙaci Meta ta yi manyan gyare-gyare, ciki har da kashe autoplay da infinite scrolling a matsayin tsarin farko, samar da ingantattun tunatarwar lokacin amfani da manhajojin, da rage yadda tsarin ba da shawarar abubuwa ke dogaro da abubuwan da ke jan hankalin masu amfani.
Meta ta ƙi amincewa da zarge-zargen na farko, tana mai cewa ta riga ta ƙaddamar da matakan kariya da dama, ciki har da Teen Accounts, ƙarfafa ikon iyaye, da wasu sabbin matakan kare matasa. Kamfanin ya ce zai mayar da martani ga Hukumar Tarayyar Turai kafin a yanke hukunci na ƙarshe.
Idan aka tabbatar Meta ta karya dokokin Digital Services Act, kamfanin na iya fuskantar tara har zuwa kashi 6 cikin 100 na jimillar kuɗaɗen shigar sa na duniya na shekara guda. Wannan shari'a na daga cikin ƙoƙarin Tarayyar Turai na ƙara ɗora wa manyan kamfanonin fasaha alhakin tasirin da manhajojinsu ke yi ga lafiyar masu amfani da kuma tsaron yanar gizo.