Kisan Dan Gwagwarmaya Dr Bala Muhammad

Yau Shekaru 45 Da Kisan Dr Bala Muhammad (Mijin Hajiya Naja’atu Muhammad) Wanda A ka Kashe A Tarzomar Siyasa a Ranar Juma'a 10 ga Yuli, 1981.

Marigayi Dr Bala Muhammad

A rana irin ta yau 10 ga watan Yuli 1981 aka kashe Dr Bala Muhammad mai bai wa Gwamna jihar Kano Alhaji Abubakar Rimi shawara akan harkokin siyasa.

Rikici tsakanin marigayi Sarki Ado Bayero da marigayi gwamnan Kano Abubakar Rimi ya kai ga sanadiyar kisan gillar da aka yiwa Dr. Bala Mohammed, matashin malami, mai kishin kasa, mai hangen nesa, mai bege da buri na samar da al'umma mai adalci da daidaito

Ya rasu yana da shekaru 35 a duniya, kuma har zuwa lokacin da aka kashe shi ya kasance mai bai wa marigayi gwamna Abubakar Rimi shawara kan harkokin siyasa a jihar Kano tsawon watanni tara.

An yi masa kisan gilla da wuta. Yayin da yake cikin aiki a cikin gidansa da ke Sultan Road, maharan marasa tsoron Allah sun banka masa wuta da sauran abubuwan da ke cikin gidan.

Marigayi Abubakar Rimi ya yi karin haske game da dalilin da ya sa aka kashe Dr Bala. In ji shi: "Abubuwan da suka faru a ranar Juma'a 10 ga Yuli abin takaici ne kamar yadda muke bakin ciki.

Amma al’amura ne da ya kamata a yi tsammani a duk wata fafutuka da za a yi tsakanin dakarun ci gaba da masu mayar da hannu agogo baya a kasar nan da ma ko’ina.”

A lokacin tarzomar ta 10 ga watan Yuli 1981 an kona majalisar dokokin Kano a lokacin ta na Hasiya Bayero dafda kofar kudu, kuma an kona gidan rediyon Kano da gidajen yan majalisar dokoki ta jiha, a lokacin su na unguwar Gwammaja, da gidan jaridar Triumph mallakar jihar Kano da sauran wurare da dama.

Post a Comment

Previous Post Next Post