Tarihin Umar Bn Said, Bakin Bawa Musulmi

A shekara ta 1807, an sace Omar bn Said, wani malami musulmi daga Senegal, aka sayar da shi bauta a Amurka. Ya bar tarihin rayuwar da aka rubuta da larabci.

Umar Bn Said

An rubuta shi da Larabci kuma kwanan nan na samu ta hanyar Library of Congress, "Rayuwar Omar Ibn Said" ba kawai labari ba ne da ba a taɓa rubutawa ba na wani Ba'amurke, amma kuma yana ɗaya daga cikin bayanan farko na tarihin Musulmai a Amurka.

Omar ya rubuta taƙaitaccen tarihin rayuwarsa, shekaru 192 da suka wuce. Lokacin da ya rubuta shi, Omar yana da shekaru 61 kuma a lokacin ya shafe fiye da shekaru ashirin a cikin bauta a Amurka, da farko yayi bauta a Charleston sannan North Carolina.

An haifi Omar bn Said a gidan hamshakan attajirai a Futa Toro, dake gabar kogin Senegal ta tsakiya a yammacin Afirka. Malamin addinin Islama ne kuma dan kabilar Fula wanda ya kwashe shekaru 25 a rayuwarsa yana karatu da manyan malaman addinin Musulunci, yana koyon lissafi, ilmin taurari da kasuwanci.

Omar ya kasance bawa kuma an kai shi Charleston South Carolina. A cikin tarihin rayuwarsa, yayi bayanin kama shi a lokacin da Turawa suka kwashe mutane da yawa" da tsallakawa dasu "babban teku" da tafiyar tsawon wata daya da rabi, ya shaida tashin hankalin cinikin bayi da ta'addanci.

Omar yana cikin kusan kashi ɗaya bisa uku na bayin Amurka waɗanda musulmi ne. Yayin da ba a san ainihin adadin musulmin da ake bautarwa ba, kusan kashi 40 cikin 100 na wadanda aka kama sun fito ne daga yankunan yammacin Afirka da galibinsu musulmi ne.

Masana sun yi kiyasin cewa jirgin bayin da ya kawo Omar zuwa South Carolina ya sauka ne a shekara ta 1807. Shekara daya bayan nan, Amurka ta soke shigowa da bayi daga ke ƙetare tekun Atlantika, wanda ya sa aka haramta shigo da sabbin bayi zuwa Amurka (ko da yake ana ci gaba da cinikin bayi ba bisa doka ba). .

Ba da daɗewa ba bayan isowarsa Charleston, Omar an sayar da shi ga wani azzalumin mai gida kuma mai tsananin tashin hankali, sai Omar ya tsere ya kama hanyarsa ta zuwa Fayetteville, North Carolina.

Da gudu Omar ya nemi wurin ibada, ya sami coci ya fara salla. Lokacin da aka nemo shi, hukumomi sun kama Omar. 

Omar Ya shahara wajen yin rubutu a bangon gidan yarin da ya zauna da harshen Larabci, inda yake kalubalantar akidar cewa ’yan Afirka da ake bautarwa ba su da ilimi.

Daga karshe wani fitaccen mutum a yankin, Janar James Owen ya siyi Omar. Saboda Sanin addinin Islama na Omar da ilimin Larabci, Owen ya ba shi Littafi Mai Tsarki na Larabci (Bible). Omar Said ya halarci Cocin Presbyterian kuma ya koma a addinin Kirista a 1821.

Daga baya Komawar Omar zuwa Kiristanci ya sa ya zama sananne. Mutane da yawa na kusa da Omar sun yi sharhi game da Kiristancinsa da kuma tsayayyen imaninsa na Kirista. Duk da haka, a cikin Littafi Mai-Tsarki, Omar ya rubuta da Larabci, "Godiya ta tabbata ga Allah, "Dukkan alheri daga Allah ne."

Ta hanyar rubuce-rubucensa, Omar ya nuna cewa yana da wayo waje ɓoye imaninsa na Musulunci. Misali, ya rubuta suratu Al Fatiha, surar farko ta Kur’ani, a cikin harshen Larabci, yana ba wa farar fata su gani.

A wani rubutu kuma, ya rubuta wani sashe na Zabura amma ya haɗa da kiran musulunci na ainihi a bayan ta. Ilimin addinin musulunci ne ya baiwa Omar damar yin amfani da harshen Larabci don boye rubuce-rubucensa na addinin musulunci. 

Omar ya koma tare da dangin Owen a 1836 zuwa Wilmington, North Carolina, kuma ya koma aikin gona a Kogin Cape Fear a lokacin Yaƙin Basasa. An yi imanin ya mutu yana da shekaru 94 a duniya, amma ba a san takamammen dalilin mutuwarsa ba.

Umar ya rubuta tafsiri da nassosi daga cikin Alkur'ani mai girma. Labarin tarihin rayuwarsa ba na tarihi ba ne, amma yana da alaƙa da muhimman abubuwan da suka faru a rayuwarsa: tilasta masa zuwa Amurka, tserewarsa da sake kama shi, da zaman da ya yi a kurkuku, da kuma tafiyarsa zuwa gidan Jim Owen.

Matsayin Omar da iliminsa a Afirka ta Yamma, da kuma tsayin daka da ya yi kan cin zarafi da ake yi masa a South Carolina, sun ba shi fasaha ta yadda zai iya samun kyakkyawar kulawa daga akalla wasu farar fata Amurkawa.

Dukansu labaran Said da tarihin rayuwarsa sun ba da labarin kyakkyawan halinsa game da karatunsa da kuma ibadarsa. A lokacin bauta ilimi, da karatu a tsakanin bayi da bai halatta ba a wasu jihohi, ciki har da South Carolina.

Musulmi bayi da suka bar rubuce-rubucen sun kalubalanci ra'ayin cewa bayi maza da mata ma'aikata ne kawai masu iya aiki na jiki saboda ba su da basirar da za su sa su cancanci 'yanci.

Abin da muka sani game da talakawan bayi Musulmi na Afirka waɗanda ba su bar rubuce-rubuce ba shi ne, za a iya tunawa da zuriyarsu da sunayensu a kan takardar siyar dasu ko sanarwar guduwarsu. Ba a san tsawon lokacin da suka yi riko da Musulunci ba

Wasu musulmin da aka bautar da su sun koma addinin kirista yayin da wasu kuma suka yi kamar sunyi ridda sun koma kirista domin gamsar da wadanda suka kama su. Amma akwai alamun cewa wasu musulmin da aka bautar da su sun yi riko da addinin Musulunci. 

'Ka ce in rubuta rayuwata…Na manta harshen Larabci da abubuwa da yawa. Haka kuma ba zan iya yin rubutu sosai da nahawu ba, don haka ya dan uwana, ina rokonka, don Allah, kada ka zarge ni, domin ni mutum ne mai raunin idanu, kuma mai raunin jiki.” "in ji Umar bn Sa'id.

Post a Comment

Previous Post Next Post