Tauraruwar Afirka: 🔥🔥🔥
Tawagar ƙasar Morocco ta lallasa ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi na gasar cin kofin duniya wato ƙasar Canada da ci 3 da nema (Cin raba ni da yaro) a wasannin zagayen 'yan 16, Ounahi da Rahimi ne suka zura ƙwallaye 3n gabaɗaya.
Duk da dagiyar da ƙungiyar ta Canada ta nuna a wasannin baya da ma wasan na jiya hakan bai hana 'yan wasan na ƙasar Morocco lallasa su tare da zuba masu ruwan ƙwallaye har 3 a raga ba.
Wannan nasara da Morocco ta samu ta ba ta damar zama ƙungiya ta farko da ta tsallake zuwa zagayen wasan na kusa da na ƙarshe (Quarter Final) Wanda ake hasashen za ta fafata da tawagar ƙungiyar Faransa. Yayin da ita kuma Canada za ta ci gaba da zama a ƙasarta domin ƙara ƙaimi wajen kula da wasannin da za a fafata har zuwa ƙarshen gasar, domin sake ɗaukar darasi.
Ya zuwa yanzu ƙasar Morocco ita ce ta fi kowace ƙasa a Afirka samun nasara a wasannin fitar da gwani (Knock out) na gasar cin kofin duniya, domin ita kaɗai ce ta samu nasara a irin wannan fage har sau 4.
Shin kuna ganin Morocco za ta iya lashe gasar kofin duniya?