A wasan da aka fafata tsakanin tawagar 'yan wasan England da ƙasar Norway a cikin daren jiya. Ingila ta samu gagarumar nasara a kan ƙasar Norway inda ta doke ta da ci 2 da 1, ƙwallayen da Jude Bellingham na ƙungiyar Real Madrid ya zura bakiɗaya.
Norway sun daɗe suna ce wa ƙungiyoyi a gasar cin kofin duniya No way, sai dai faɗin hakan ga ƙungiyar Turawan Ingila ya faskara, duk da namijin ƙoƙarin da suka yi don ganin sun kawar da Ingilar a gabansu, amma hakan bai yiwu ba.
Yanzu dai Belgium sun gama tallata kawunansu da ƙungiyarsu a gasar cin kofin duniya, sai kuma a koma gida da ɗan abin da aka samu a jalaulauta, tare da sake sabon shiri zuwa shekaru huɗu masu zuwa ga mai yawancin kwana.
Haka nan, Ingila ta kawo ƙarshen takarar ɗan wasan ƙwallon gaba na Norway Erling Halland na neman zama zakaran ɗan wasan da ya fi sura ƙwallaye a gasar, ya zuwa yanzu Haaland yana da ƙwallaye 7 a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Su kuwa Turawan Ingila za su fafata ne da ƙasar Argentina a gasar cin kofin duniya matakin kusa da na ƙarshe (Semi Final).