Da tsakar daren jiya ƙungiyar ƙwallon ƙafar Argentina ta yi wa takwarata ta ƙasar Switzerland ƙarfa-ƙarfa inda ta doke ta da ci 3 da 1.
Masana kallon wasanni da masharhanta da kuma wasu daga cikin 'yan adawa ta Sarki Messi sun nuna shi ma wannan wasan an ba wa tawagar ta Argentina damar ta ci gaba da haskawa ne kawai ba wai ƙarfinsu ne ya ci masu wasan ba. Sun dake da kan katin da aka ba wa ɗan wasan gaba na ƙasar Switzerland a mintina na 74 wanda hakan ya sa Argentina ta doke su a cikin ƙarin mintinan 30 da aka yi.
Sai dai a wani ɓangaren kuma, idan aka yi duba da laifin Embolo ya kamata a gane ya cancanci wannan katin, sai dai ka san ba yadda ka iya da wanda ba ya son ka. Haka aka dinga yaɗa maganganu kan an zalunci Egypt, Amma da shugaban alƙalan wasanni Collins ya zo sai ya nake filin tare da Bayyana cewa abin da aka yi wa Salla bai kai a hura shi a matsayin foul ba. Duk da shi ma bai tsallake kalmomin cin mutuncin ga waɗanda ba sa don Messi ɗin da ƙungiyarsa ba.
Ƙungiyar Argentina za ta fafata da ƙungiyar England a wasan daf da na ƙarshe. Lallai za a sha kallo, domin dai akwai daɗaɗɗiyar hamayya a tsakanin ƙungiyoyin biyu.