Tsohon Sufeto Janar Na Yan Sandan Nijeriya A Jihar Jigawa Ya Fice Daga Jam'iyyar APC Zuwa PDP

Tsohon Sufeto Janar na 'yansandan Najeriya, Suleiman Abba, ya fice daga jam'iyyar APC tare da komawa PDP a Jihar Jigawa.

Suleiman Abba

Abba ya sanar da sauya sheƙarsa ne a wani taron gangami da aka gudanar a Bamaina, mahaifar tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, inda shugabannin PDP da magoya baya suka tarbe shi.

Ya bayyana cewa ya koma PDP ne domin neman takarar Sanatan Jigawa ta Kudu maso Yamma a zaɓen 2027, yana mai cewa zai mayar da hankali kan inganta tsaro, noma da samar da ayyukan yi ga matasa.

A nasa bangaren, Sule Lamido ya ce shigowar Abba babbar nasara ce ga PDP, yana mai cewa hakan zai ƙarfafa jam'iyyar kafin babban zaɓen 2027.

Shi ma shugaban PDP na Jigawa, Babandi Gumel, ya tabbatar da cewa jam'iyyar ta shirya karɓar Abba da dubban magoya bayansa cikin tsarinta a faɗin jihar, yayin da ɗan takarar gwamnan PDP a Jigawa, Mustapha Lamido, ya ce sauya sheƙar Abba zai ƙara wa jam'iyyar ƙarfi a jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post