Gwamnatin Iran ta ayyana ranar Lahadi, 5 ga Yuli, a matsayin ranar hutu a faɗin ƙasar domin bai wa jama'a damar halartar jana'izar da zaman makokin Ayatollah Ali Khamenei.
A cewar gwamnati, an ɗauki matakin ne bayan buƙatu da dama daga larduna daban-daban na ƙasar da suka nemi a ba mutane damar shiga bukukuwan jana'izar tsohon jagoran addinin ƙasar.An fara jana'izar ne a yau Asabar a birnin Tehran kuma ana sa ran za ta ci gaba har zuwa ranar 9 ga Yuli, tare da halartar dimbin masu makoki daga sassa daban-daban na ƙasar.
Rahotannin kafafen yaɗa labaran Iran sun ce Ayatollah Jafar Sobhani Tabrizi ne zai jagoranci sallar jana'izar Khamenei da za a gudanar a harabar Mosalla da ke Tehran da safiyar Lahadi.