Dubban mutane sun fito zanga-zanga a sassa daban-daban na Germany domin nuna adawa da jam’iyyar Alternative for Germany (AfD) mai ra’ayin dama, yayin da jam’iyyar ke gudanar da babban taronta.
Masu zanga-zangar sun yi tattaki dauke da alluna da tutoci, suna kira da a kare dimokuraɗiyya, haƙƙin ɗan adam da kuma nuna adawa da manufofin da suke zargin jam’iyyar na haifar da rarrabuwar kawuna da nuna wariya.
A nata ɓangaren, jam’iyyar AfD ta ci gaba da gudanar da taronta, inda shugabanninta suka tattauna kan manufofinsu game da shige da fice, tattalin arziki da sauran batutuwan siyasa. Jam’iyyar ta ce tana wakiltar muradun masu kaɗa ƙuri’a da ke neman sauye-sauye a manufofin gwamnati.
Hukumomin tsaro sun tura jami'an 'yan sanda da dama domin tabbatar da zaman lafiya tare da hana rikici tsakanin masu zanga-zanga da magoya bayan jam’iyyar. An ce zanga-zangar ta gudana lafiya a yawancin wurare, duk da samun ƙananan rikice-rikice a wasu yankuna.
Zanga-zangar ta sake nuna irin yadda jam’iyyar AfD ke ci gaba da raba ra’ayin jama'a a Jamus, inda wasu ke kallonta a matsayin babbar jam’iyyar adawa, yayin da wasu ke nuna damuwa kan tasirin manufofinta ga siyasa da zamantakewar ƙasar.