Mutane 11 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Edo Sun Gudu Bayan Da Barci Ya Kwashe Yan Bindiga

Mutane 11 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Etsako West ta jihar Edo sun tsere daga hannun masu garkuwar bayan da ake zargin maharan sun yi barci sakamakon gajiya bayan tafiya cikin daji tsawon dare.

Jihar Edo

Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, Destiny Braimah, ya ce an sace su ne yayin da yake dawowa daga gona tare da wasu mutum 10, inda aka tilasta musu yin tafiya cikin daji. 

Ya ce bayan sun ji harbe-harben da ake zargin 'yansanda ne suka yi, maharan sun ɓuya sannan suka yi barci, lamarin da ya ba su damar tserewa zuwa ofishin 'yansanda.

Wata da aka sace a baya, Gloria Inyanugbo, ta ce ta shafe kwanaki huɗu a hannun masu garkuwar kafin mijinta ya biya naira miliyan uku domin a sake ta, kuma ta gane wasu daga cikin maharan bayan kama su.

A halin da ake ciki, rundunar 'yansandan jihar Edo ta ce ta kama mutane 32 da ake zargi da garkuwa da mutane a watan Yuni tare da ceto mutum 38 a hare-haren da ta gudanar a faɗin jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post