An bayyana marigayi Kanal Abdulsalam Ude na hukumar leken asirin sojojin Najeriya (DIA), wanda aka kashe bayan ya yi ƙoƙarin hana wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sace shi a gidansa da ke Abuja, a matsayin malamin Alƙur'ani kuma ƙwararren masani a harshen Larabci.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:45 na daren Litinin bayan jami'in ya isa gidansa da ke Phase 5 na Army Housing Estate, Kurudu, a wajen birnin Abuja.
Jaridar TheCable ta rawaito cewa wani mai amfani da shafin X mai suna Uthman Isa Tochukwu ya ce rasuwar Kanal Ude babban rashi ne ga Musulman Igbo da ma Najeriya baki ɗaya.
A cewarsa, marigayin ya kasance Hafizul Alƙur'ani ne, kuma yana da cikakken ƙwarewa a harshen Larabci, tare da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun jami'an leken asirin soja a ƙasar.
Tochukwu ya ƙara da cewa ana sa ran za a ƙara masa girma zuwa mukamin Birgediya Janar a shekara mai zuwa, wanda a cewarsa babu wani Musulmin Igbo da ya taɓa kai wa wannan matsayi a aikin soja.
Ya bayyana cewa marigayin ya samu lambobin yabo da dama saboda ƙwarewarsa a fannin leken asiri da tsaro, sannan ya kasance mutum mai natsuwa da tawali'u wanda ya sadaukar da kansa wajen koyar da Alƙur'ani da tarbiyyar matasa.
Shi ma wani mai amfani da shafin X, Aminu Baban Mairam, ya bayyana Kanal Ude a matsayin mutum na musamman, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga Najeriya ba tare da la'akari da addini ko ƙabila ba.
Haka kuma, Salahuddeen Ibn Gauss ya ce mutuwar Kanal Ude ba ta shafi Musulman Igbo kaɗai ba, illa ta shafi al'ummar Musulmi gaba ɗaya.
