A rana mai kamar ta yau 27 ga watan Yuli 1903 (Yau Shekaru 123) kenan: Sojojin mulkin mallaka na Birtaniya suka kashe Sultan Muhammadu Attahiru a Burmi, wanda hakan ya nuna rugujewar Khalifancin musulunci a Sakkwato.
Yaƙin Burmi wanda aka kashe sarkin musulmi Muhammadu Attahiru 1
Yakin Burmi shi ne yakin karshe tsakanin Turawan mulkin mallaka da sojojin Daular Sakkwato. Yakin ya zo ne bayan nasarar da Ingila ta samu a yakin Kano da Kwatarkwashi, wanda ya tilastawa mayakan Sokoto ja da baya a fadin Arewacin Najeriya, inda suka koma Burmi. A lokacin kwamandan yaki na sojojin Birtaniya Manjo Marsh da kuma Halifan Sokoto, Muhammadu Attahiru na I duk aka kashe su.
Bayan kama garin Sakkwato da turawan mulkin mallaka na Ingila suka yi a ranar 15 ga Maris 1903, Halifan Sakkwato Muhammadu Attahiru ya gudu tare da dimbin mabiya. Nufinsa shi ne ya yi hijira zuwa Makka maimakon ya ci gaba da zama a karkashin mulkin Birtaniya. Yayin da yake yunƙurin gujewa kamun Turawan mulkin mallaka, Halifa ya ratsa garuruwa da kauyuka da dama, yana jawo hankalin mabiyan da zai haɗa da nufin yin hijira, a cikin birane da kauyuka, akalla rabin al'ummar yankunan da ya ratsa sun shiga cikin tafiyar sa.
Turawan Ingila sun ci gaba da bin bayansu domin su kama Attahiru ko kuma su kashe shi, amma sun kasa cim masa. A yayin bin bayan nasa, sojojin Birtaniyya sun kashe akalla mutane 35 da suke yunkurin shiga cikin tawagar Halifa. Sun ci gaba da bibiyar sa har zuwa garin Burmi da ke masarautar fukanaye ta jihar gombe ta yau, a ranar 13 ga watan Yuni 1903.
Burmi dai na karkashin ikon Burtaniya ne. Sai dai bayan da turawan Ingila suka nada sarkin garin sai ya ki bin umarninsu, sai suka kai hari garin. Hare-haren dai ya janyo hasarar da dama ga dakarun Burmi, inda Sarki garin na cikin wadanda aka kashe. Duk da nasarar da suka samu, Birtaniya sun kasa shiga garin saboda harbin kibiya mai karfin gaske da masu kare garin suka yi. Daga karshe dai suka yanke shawarar janyewa zuwa Bauchi "don kada 'makiya' su samu nasara a yaki su gama da su."
Birtaniyya ta yi asarar sojoji biyu da aka kashe, sannan hamsin da shida suka samu raunuka, yayin da ‘yan Burmi suka yi asara mai yawa, inda aka kashe akalla mutane 150, an ba da rahoton cewa gawarwakinsu na kwance a gaban kofar garin.
Kwamandan Birtaniya a Gujba ta lardin Bornu, Kyaftin Hamilton Browne, ya samu labarin cewa Attahiru ya isa Bima kusa da Gwoni, kimanin tafiyar mil 30 yamma da Gujba. Nan da nan Browne ya bar Gujba tare da wani kwamandan soja daya da sojojin haya 51, da kuma bindigogi Maxim. Daga karshe dai sun isa Gwoni a ranar 17 ga watan Mayu. Da ganin sansanin Attahiru, sai suka bude musu wuta da bindigar Maxim da sauran wasu bindigu. Sai mabiyan Halifa suka gudu suka haye kogin Gongola zuwa yamma, suka bar “dukkan kayansu da bindigu 63 da harsasai masu yawa, da rakuma da dawakai da jakuna da yawa.” Attahiru ya ja da baya ya nufi Burmi.
Bayan da ya sami labarin koma bayan da Birtaniya ta samu, sai Browne ya koma Gujba. A daidai wannan lokaci, Manjo Barlow, wani jami'in Birtaniya, ya bar Zariya tare da wasu jami'an Birtaniya guda biyu da wasu sojojin haya 60. Ya isa Gombe ne a ranar 23 ga watan Mayu, da samun labarin kasancewar Attahiru a Burmi, sai ya tashi don kama Halifa, a ranar 26 ga watan Mayu, a ranar 31 ga Mayu, Barlow tare da ‘yan sintiri suka mamaye garin Ashaka da ke gabar kogin Gongola, amma masu tsaron garin sun yi musu mummunar barna.
Tare da wannan hadin gwiwar sojojin, Barlow "ya ci gaba da kewaye garin Burmi ba tare da yunkurin shiga garin da karfi ba." Tun daga ranar 4 ga watan Yuni, Barlow ya aiwatar da killace Burmi, "ya hana kai shanu da kayan abinci" da ake aikawa daga Bauchi. Bayan kamar sati biyu, mutanen Burmi, sun fusata sosai, suka fito don kai hari ga turawan Ingila da suka yiwa garin kawanya. Daga karshe dai an fatattake su bayan wata dogon fada da aka yi, inda aka kashe 18 daga cikinsu.
Yaƙi
An fara yakin ne da karfe 11 na safe ranar Juma’a 27 ga watan Yulin 1903, inda sojojin Birtaniya suka yi ta luguden wuta a garin Burmi. Bayan harin da aka kai a garin, Burtaniya ta kaddamar da harin gaba da gaba a garin, wanda Manjo Charles Marsh ya jagoranta da kansa, dakarun Burmi suka harbe shi da kibiya mai guba. Marsh ya mutu bayan kimanin mintuna 20, yayin da ake ci gaba da gwabzawa.
Sojojin Birtaniya da sojojin Burmi sun yi mugun gumurzu ta inda daga karshe suka samu nasara a kan sauran masu tsaron sarkin musulmi Muhammadu Attahiru I kuma suka kashe shi. A cewar rahotanni na Birtaniya, "bindigu kirar Maxim sun yi kisa da yawa" kuma a kalla" an kashe mutane sama da 600 tare da kone garin." An tsinci gawar Attahiru kwance a karkashin gawarwakin mabiyansa 90.
Har yanzu kabarin Sarkin musulmi Attahiru 1 da Manjo Charles Marsh su nan burmi, a yanzu garin ya zama kufai ba kowa.
