A Karon Farko Manchester United ta Doke Atlantico Madrid

A karon farko, Manchester United ta samu nasara a kan ƙungiyar Atlantico Madrid da ke Sifaniya a wasannin sada zumunci da aka fafata da misalin ƙarfe 2 na ranar yau Asabar.

A wasan sada zumunci da ake fafatawa domin lashe kofin Snapdragon, Manchester United ta lallasa Atlantico Madrid da ci 2 da 1. Wanda wannan shi ne karo na farko da ƙungiyar ta Manchester United ta taɓa yin nasara a kan ƙungiyar a cikin wasanni 4 da suka taɓa goge raini. Wanda a ciki Atlantico ta samu nasarar doke Man Utd sau biyu da cin kwallo ɗaiɗaya a kowanne wasa da suka yi nasara; wasa ɗaya a gasar cin kofin Turai (Champions League), sai kuma ɗayan a wasan sada zumunta irin na yau, sai kuma wasa ɗaya da suka yi canjaras 1 da 1, shi ma a gasar cin kofin zakarun Turai.

Nasarar da Manchester United ta samu a yau, inda ya doke AT Madrid da ci 2 da 1, ya ba ta damar sake lashe kofin Snapdragon sau 3 a jere.

Duka ƙwallaye biyun, Bryan Mbuemo ne ya zura su, ɗaya ta bugun daga kai sai mai tsaron raga, ɗayar kuma ana tsaka da wasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post