Alamomin Da Ke Nuna Cewa Kai Lafiyayyen Namiji Ne

1. Samun Cikakken Kuzari Da Safe (Healthy Morning Erection).

Namiji

Wannan ita ce babbar alamar farko  dake nuna lafiyar namiji.

 dan kana farkawa da safe ka sami kanka cikin cikakken kuzari.

Wannan yana nuna cewa sinadarin mazantakarka  na Testosterone yana matakin da ya dace, kuma jijiyoyin jinin ka suna tura jini zuwa kowane sashe na jikinka cikin sauki. Idan wannan dabi'ar ta ɓace na tsawon lokaci, yana iya zama alamar farko na Hawan Jini ko ciwon suga na ɓoye.

2.Baka da matsala da gudun fitsari(Normal Urine Flow) 

Idan ka shiga banɗaki, fitsarinka yana fitowa ne nan take da ƙarfi ba tare da ka shafe lokaci  kana jinkiri ko matse ciki ba domin fitsarin yafito, kuma kalar fitsarin ka yana da haske ko yellow mai haske (Clear/Pale yellow).

 Wannan yana nuna cewa kodarka tana tace guba da kyau, kuma ba ka da alamun kumburin Prostate ko Ciwon sanyin Fitsari (UTI).

3.Farka Da Safe Cikin Kuzari Ba Tare Da Kasala Ba 

 Bayan ka yi wadataccen barci na sa'o'i 7 zuwa 8, za ka tashi da safe ka ji jikinka sakayau,kaji ka huta.

Wannan yana nuna cewa jikinka yana sarrafa abinci kuma ya magana dashi yadda ya kamata, kuma ba ka da matsalar Qarancin Jini (Anemia),ciwon zuciya,koda,hanta,ciwon siga ko wata matsala daban

4. Rashin Saurin Fusata (Emotional Stability & Focus)

Idan kana da juriya da ikon fuskantar matsalolin rayuwa ko na kasuwanci cikin natsuwa, ba tare da ka riƙa shiga damuwa ko fushi ko tsoro ba, kuma kana iya mayar da hankali akan aiki guda ɗaya na tsawon lokaci.

Wannan yana nuna cewa sinadaran ƙwaƙwalwarka irin su Serotonin da Dopamine suna wadace, kuma ba ka da alamun ciwon damuwa (Depression)

Likita24

Post a Comment

Previous Post Next Post