An Kashe 'Yan Sandan 10, Yayin Da Suka Kashe 'Yan Ta'adda Sha Bakwai A Wani Bata Kashi A Jihar Kebbi

Bayan samun rahoton fitowar 'yan ta'adda daga yankin Zamfara a jiya Litinin, waɗanda suka yi kaciɓus da jami'an tsarommu na 'yansanda, inda suka yi ta musayar wuta ba ƙaƙautawa.

A yau Talata rundunar 'yansandan Najeriya ta fitar da sanarwar mutuwar jami'anta goma (10) a wannan artabu da 'yanbindiga da suka yi a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya a jiya Litinin.

Rundunar ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar jiya Litinin 10 ga watan Agusta, a yankin ƙauyen Rafin Makuku da ke ƙaramar hukumar Sakaba, jihar Kebbi.

A sanarwar da kakakin rundunar na ƙasa CSP Ani Iniedu ya fitar, ya ce jami'an 'yan sandan sun tare 'yanbindigar ne waɗanda suke ɗauke da manyan makamai yayin da suke ƙoƙarin wucewa daga jihar Zamfara zuwa Kebbi, inda suka yi musayar wuta. Rundunar ta ce ma'aikatanta sun kashe aƙalla 'yanbindiga 17 tare da lalata babura huɗu na maharan, wanda aka ce an hango ɓarayin dajin ɗauke da gawarwakin abokan nasu a saman babura 17.

Sai dai a yayin wannan musayar wuta ma'aikatan 'yansanda goma (10) ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka inda a yanzu suke samun kulawa a asibiti.

Rundunar 'yansandan ta ƙara da cewa, bayan 'yansanda 10, an kuma samu wasu fararen hula guda biyu da abin ya rutsa da su, waɗanda suka rasa rayukansu yayin artabun.

Wannan hoton na daga cikin kayan da ɓarayin dajin suka lalata a yayin musayar wutar.

Post a Comment

Previous Post Next Post