"Ban Ga Dalilin Tayar Da Jijiyar Wuya Ba Don Rarara Ya Yi Wa Pantami Zambo" Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam'iyyar NDC, kuma shugaban kwankwasiyya Eng. Dr Rabi'u Musa Kwankwaso a firarsa da ya yi da gidan talabijin na DCL Hausa. Ya bayyana cewa, Rarara ba yau ya fara zargin mutane a waƙa ba, domin har shi bai raga masa ba, ya kiraye shi da suna kala-kala duk da bai ambaci sunayen da ya kira shi da su ba. 

Kwankwasi ya ƙra da cewa, ba iya shi kaɗai ba, hatta Ganduje Rarara ya yi wa waƙoƙin taɓa kima, to shi bai ga dalilin da zai sa mutane su yi caaaa suna ta faɗin maganganu don an yi wa Pantami Zambo ba. Tunda har Pantami ya shigo siyasa ya sani wannan wani yakushi ne da aka fara yi masa.

Eng Rabi'u Musa ya ce, a baya can kafin malam ya shiga siyasa shi ma mene ne bai faɗa a kan 'yan siyasar ba, idan maye ya manta ai uwar ɗiya ba ta manta ba. Nan ya yi min tas a mimbari, har watarana nan aka zo za a yi mashi duka irin na 'yan siyasa na hana. 

Bayan ma wannan, shi malam ai yana cikin jarabawa, mene ne bai faɗa a kan siyasa ba, dubi dai jam'iyyar da yake takara a cikinta, jam'iyya kafira ya kira ya, yanzu ga shi a cikin kafirar jam'iyya.

Post a Comment

Previous Post Next Post