A Jiya Litinin 10/ 08/2027 Darakta Janar, Yaɗa Labarai da Watsa Labarai, Fadar Gwamnati, Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar da sanarwar cewar, Gwamnan jihar Kano Maigirma Alhaji Abba Kabir Yusuf Ya Amince Da Ƙarin Albashi Ga Ma’aikatan Jami’o’i Biyu Na Jihar Kano.
Bature ya bayyana cewa, maigirma Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin bita na albashi ga Ma’aikatan Ilimi da waɗanda ba a Ilimi ba na Jami’ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha, da ke Wudil, da kuma na makarantar Jami’ar North West da ke Kano.
Mai maganar ya ce, wannan Sabon ƙarin albashin an ɗauko tsarin ne ne daga sabon tsarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta aiwatar a Jami’o’in Tarayya na Najeriya.
Amincewar gwamnan, ta biyo bayan bayyanar rahoto da kuma shawarwarin da kwamitin da Majalisar Zartarwa ta Jihar ta kafa domin bincike da kuma sake nazarin buƙatar jami’o’in biyu, na gwamnatin jihar domin aiwatar da sabon tsarin albashin.
A bisa sabon tsarin da aka amince da shi, sabon tsarin albashin zai fara aiki daga watan Janairu 2026, yayin da biyan kuɗin zai fara a watan Satumba 2026.
Bayan sake duba fasalin albashin abin da za a bayar zai kai jimillar kuɗi ₦391,847,555.24 a kowane wata, wanda ya kai ₦4,702,170,662.88 a duk shekara ga jami’o’i biyun.
Ga yadda tsarin zai kasance:
Jami’ar Kimiyya da Fasaha, Ta Aliko Dangote da ke Wudil: Jimillar kowane wata ₦228,195,210.83 ₦141,082,223.37 na Ma’aikatan Ilimi ƙarƙashin yarjejeniyar ASUU sai kuma ₦87,112,987.46 na Ma’aikatan da ba na ilimi ba ƙarƙashin SSANU
Sai kuma Jami’ar North West, Kano: Jimillar kowane wata ₦163,652,344.41 sai kuma ₦112,238,985.30 na Ma’aikatan Ilimi da kuma ₦51,413,359.11 na Ma’aikatan da ba na ilimi ba
Gwamnatin Kano ta amince a saka ₦1,567,390,220.96 a cikin kasafin kuɗi na 2026 na ƙari domin biyan kuɗin daga Satumba zuwa Disamba 2026. Hakazalika, bashin baya na daga watan Janairu zuwa Agusta 2026, wanda ya kai ₦3,134,780,441.92, za a saka shi a cikin kasafin Kuɗi na 2027.
Rahoton kwamitin ya bayyana cewa, an ɗauki wannan mataki ne da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma’aikata da kuma inganta walwalarsu, daidai da yadda aka aiwatar da sabon tsarin albashi a jami’o’in tarayya da sauran jami’o’in jihohi.
Gwamna Abba ya kuma amince da kafa Kwamitin bincike na ziyara ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, kamar yadda doka ta tanada, domin ƙara ƙarfafa gaskiya da gudanarwa domin samun ingantattun hanyoyin sarrafa makarantun.
Gwamnan ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na inganta walwalar ma’aikata da haɓaka ingancin ilimin gaba da sakandare, a matsayin wani ɓangare na babban zuba jari a ci gaban ɗan'adam.