Shayin da ake haɗawa daga ganyen zaitun (olive leaf) da zogale (moringa) suna ƙara samun karɓuwa a tsakanin masu kula da lafiyarsu, sakamakon amfanin da ake ganin zai iya yi wa jikin ɗan Adam. Masana harkar abinci mai gina jiki sun bayyana cewa wannan shayi na ɗauke da sinadarai masu hana lalacewar ƙwayoyin halitta (antioxidants), bitamin da wasu muhimman sinadarai na tsirrai da ka iya taimakawa wajen inganta lafiyar jiki idan aka sha cikin matsakaici.
Ganyen zaitun na ɗauke da wani sinadari mai suna oleuropein, yayin da ganyen moringa ke ƙunshe da bitamin, ma’adanai da sinadarai masu hana lalacewar ƙwayoyin halitta. Waɗannan sinadarai na iya taimakawa wajen kare ƙwayoyin jiki daga lalacewar da ke faruwa sakamakon abin da masana ke kira oxidative stress, wanda ake dangantawa da tsufa da kuma wasu cututtuka masu ɗorewa.
Masu bincike a fannin lafiya sun nuna cewa shan shayin ganyen zaitun da na zogale a-kai - a-kai na iya taimakawa wajen inganta lafiyar zuciya ta hanyar tallafa wa kyakkyawan zagayawar jini da kuma taimakawa wajen daidaita hawan jini ga wasu mutane. Haka kuma, shayin na iya ƙarfafa garkuwar jiki saboda sinadarai masu amfani da ke cikin ganyen zogale .
Bugu da ƙari, wasu bincike sun nuna cewa moringa na iya taimakawa wajen daidaita yawan sukari a jini, yayin da sinadarai da ke cikin ganyen zaitun ke da kaddarorin rage kumburi da kuma hana lalacewar ƙwayoyin halitta. Duk da haka, masana sun yi gargaɗin cewa har yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan haɗin ganyen zaitun da moringa, don haka bai kamata a ɗauki wannan shayi a matsayin maganin cutar sukari, hawan jini ko wasu cututtuka ba.
Haka kuma, wannan shayi na iya ƙara wa jiki kuzari da wasu muhimman sinadarai masu gina jiki, domin moringa na ɗauke da bitamin da ma’adanai da ke taimakawa wajen gudanar da ayyukan jiki yadda ya kamata.
Masana lafiya sun ba da shawarar a rika shan shayin cikin matsakaici, wato kofi ɗaya zuwa biyu a rana. Sun kuma shawarci mutanen da ke amfani da magungunan cutar sukari, hawan jini ko magungunan rage kaurin jini da su tuntubi ƙwararren likita kafin su rika amfani da wannan shayi akai-akai.
Ko da yake shayin ganyen zaitun da zogale na iya kasancewa da wasu fa’idodi ga lafiya, masana sun jaddada cewa mafi kyawun sakamako yana samuwa ne idan an haɗa amfani da shi da cin abinci mai gina jiki, motsa jiki akai-akai, samun isasshen barci da kuma bin shawarwarin likitoci idan buƙatar hakan ta taso.
Saboda haka, ana iya kallon shayin ganyen zaitun da zogale a matsayin wani abin sha da zai iya taimakawa wajen inganta lafiyar jiki, amma bai kamata ya maye gurbin magungunan da likita ya rubuta ko kuma kulawar ƙwararrun ma’aikatan lafiya ba.