An Yi Shekara 81 Da Kasar Amurka Ta Jefa Bom Din Nukiliya A Birnin Nagasaki Na Kasar Japan

A ranar 9 ga watan Augusta 1945 a Yaƙin Duniya na Biyu: Birnin Nagasaki ya lalace, lokacin da jirgin yakin Amurka B-29 Bockscar ya jefa bam din Atomic Na Nukiliya mai suna (fat man).

Nagasaki

A cewar wani rahoto na yankin Nagasaki "mutane da dabbobi sun mutu kusan nan take!.

A ranar 6 da 9 ga watan Agustan 1945 ne Amurka ta tayar da bama-baman nukiliya guda biyu a kan garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan. Hare-haren bama-bamai guda biyu sun yi sanadiyyar mutuwar mutane tsakanin 129,000 da 226,000, wadanda akasarinsu fararen hula ne.

Birnin Nagasaki ya kasance daya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa a kudancin kasar Japan, kuma yana da matukar muhimmanci a lokacin yaki saboda yawan ayyukan masana'antu, da suka hada da kera makamai, jiragen ruwa, kayan yaki, da sauran kayayyakin yaki. Kamfanoni hudu mafi girma a cikin birnin sun hada da Mitsubishi Shipyards, Electrical Shipyards, Arms Plant, Steel and Arms Works, wanda ke daukar kusan kashi 90 cikin 100 na ma'aikatan birnin, kuma sun kai kashi 90 na masana'antar birnin.

Post a Comment

Previous Post Next Post