Amurka na shirin ƙara tsaurara takunkuman tattalin arziƙi kan Iran, matakin da Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya kira “economic D-Day” wato gagarumin yaƙin tattalin arziƙi da nufin matsawa Iran lamba sosai.
Babban ƙalubalen shi ne China, domin ita ce babbar mai sayen man fetur daga Iran. Amurka na barazanar amfani da secondary sanctions, wato hukunta kamfanoni, bankuna ko ƙasashen da ke ci gaba da kasuwanci da Iran. Wannan na iya shafar kamfanonin China kai tsaye.
Wannan ne yake gwada abin da ake kira “China detente” ƙoƙarin Trump na rage tashin hankali da Beijing da kuma inganta dangantakar Amurka da China. Idan Washington ta matsa wa kamfanonin China da ke sayen man Iran lamba, hakan na iya sake haifar da rikicin tattalin arziki tsakanin manyan ƙasashen biyu.
China ta riga ta nuna rashin amincewa da irin waɗannan takunkuman Amurka, tana mai cewa matakan da ƙasa ɗaya ke ɗauka ba tare da amincewar ƙasa da ƙasa ba ba su dace ba. Saboda haka, Trump na fuskantar zaɓi mai wahala: ko ya ƙara matsawa Iran lamba, ko kuma ya yi taka-tsantsan don kada ya lalata sabuwar dangantakar da yake ƙoƙarin ginawa da China.