Bashin Amurka ya Haura Hala Tiriliyan 40


Bashin ƙasar Amurka ya haura dala tiriliyan 40, kamar yadda bayanan gwamnati suka nuna a ranar Laraba. Wannan adadi ya zarce hasashen da aka yi a baya, inda ƙarin bashin ke faruwa a wani ɓangare sakamakon tasirin harajin kwastam da Shugaba Donald Trump ya kakaba, wanda daga bisani aka soke.

Bayanan Ma’aikatar Baitulmalin Amurka sun nuna cewa jimillar bashin gwamnati ya kai dala tiriliyan 40.05 a ƙarshen kasuwancin ranar Talata.

Wannan adadi ya zarce hasashen Ofishin Kasafin Kuɗin Majalisar Dokokin Amurka (CBO), wanda ya yi hasashen cewa bashin ƙasar zai kai dala tiriliyan 39.4 ne kawai a ƙarshen shekarar kasafin kuɗi ta 2026.

Ƙarin bashin Amurka na zuwa ne a lokacin da kuɗaɗen da gwamnati ke warewa domin biyan wajibcinta na dogon lokaci, musamman na Social Security da kiwon lafiya, ke ƙaruwa. Haka kuma, kuɗin ruwa da ake biya kan basussukan ƙasar na ci gaba da hauhawa.

Ƙarin bashin ya zo ne a wani lokaci mai cike da damuwa, yayin da farashin karɓar bashi ke ƙaruwa.

A ranar Talata, ribar da ake samu daga dogayen takardun bashin gwamnatin Amurka ta haura zuwa matakin da ba a taɓa gani ba tun shekarar 2007. Wannan na faruwa ne sakamakon fargabar hauhawar farashi da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke haifarwa, da kuma damuwar da ake da ita kan yawan gibin kasafin kuɗin Amurka.

Wannan yanayi ya tilasta wa gwamnatin Amurka sake tsara wasu daga cikin basussukanta da mafi tsadar kuɗin ruwa tun kafin rikicin kuɗi na duniya na shekarar 2008.

Sai dai Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta ɗauki matakan da nufin daidaita kasuwar dogayen takardun bashi a safiyar Laraba, lamarin da ya sa ribar takardun bashin ta ragu.

Gwamnatin tarayyar Amurka tana kashe kuɗaɗe fiye da abin da take samu, don haka take karɓar bashi domin cike gibin da ke tsakaninsa da kuɗaɗen shigarta.

Jessica Riedl, masaniya kan kasafin kuɗi da haraji a Cibiyar Brookings, ta ce an daɗe da sanin cewa gwamnatin Amurka tana tafiya ne a kan hanyar da ba za ta iya ɗorewa ba saboda yawan gibin kasafin kuɗinta.

Ta ce a cikin ƴan shekarun nan, Amurka tana fuskantar gibin kasafin kuɗi na kusan dala tiriliyan biyu a kowace shekara, har ma a lokacin da ƙasar ba ta cikin yaƙi kuma tattalin arzikinta ke cikin yanayi mai kyau.

Riedl ta ce a baya, gibin kasafin kuɗi da ya kai kashi uku zuwa huɗu cikin ɗari na GDP kan jawo damuwa a kasuwannin kuɗi. Amma yanzu gibin ya kusanci kashi shida zuwa bakwai cikin ɗari na GDP.

“Wannan ya sa kasuwannin kuɗi suka ƙara shiga damuwa,” in ji ta.

Post a Comment

Previous Post Next Post