Fadar Shugaban Najeriya ta caccaki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, kan alkawarinsa na dawo da tallafin man fetur idan ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa mai zuwa.
Mai Bai wa Shugaban Kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce matakin na Atiku ya nuna sauya matsaya kan wani muhimmin bangare na manufofin tattalin arzikinsa da ya gabata.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Onanuga ya ce Atiku ya bayyana goyon bayan cire tallafin man fetur a lokacin yakin neman zabensa na 2023, amma yanzu ya sauya matsayinsa saboda neman samun karbuwa a wajen masu kada kuri’a.
Ya ce alkawarin dawo da tallafin ba zai kasance abu mai sauki ba, domin dokar Petroleum Industry Act (PIA) ta tanadi kawo karshen tsarin tallafin man fetur tun daga karshen watan Yunin 2023.
Onanuga ya bayyana cewa tallafin ba wai wasu kudade ne da suke a taskar gwamnati domin a rabawa jama’a ba, illa tsarin da gwamnati ke biyan gibin da ke tsakanin kudin da ake sayen man fetur da farashin da ake sayar da shi ga jama’a.
Ya ce a baya wannan tsari ya janyo wa gwamnati asarar makudan kudade tare da kara dogaro da bashi wajen tafiyar da harkokin tallafin.
“Idan aka dawo da tallafin, tambayar da ya kamata ‘yan Najeriya su yi ita ce: wa zai biya kudin?” in ji shi.
Mai bai wa shugaban kasa shawarar ya ce idan za a sayar da man fetur kasa da ainihin kudinsa, dole ne gwamnati ta dauki nauyin gibin, lamarin da zai iya rage kudaden da ake warewa ayyukan more rayuwa da sauran hidimomin jama’a ko kuma kara yawan bashin kasa.
Ya kuma ce yanayin bangaren man fetur a Najeriya ya sauya matuka tun bayan cire tallafin, musamman saboda karuwar samar da man fetur a cikin gida.
A cewarsa, matatar man fetur ta Dangote da sauran matatun cikin gida sun kara samar da man fetur a Najeriya, abin da ya rage dogaro da shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje.
Onanuga ya ce dawo da tsohon tsarin tallafin na iya kawo cikas ga ci gaban matatun cikin gida tare da rage jarin da ake samu a bangaren.
Ya kara da cewa kudaden da gwamnati ta daina kashewa wajen tallafin sun kara yawan kudaden da ke zuwa ga matakan gwamnati uku ta hanyar rabon kudaden asusun tarayya.
Ya ce a watan Yuli kadai, gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi sun raba kusan Naira tiriliyan uku daga asusun tarayya, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin nasarorin cire tallafin man fetur da kuma sauye-sauyen tsarin musayar kudaden kasashen waje.
Sai dai ya amince cewa karin farashin man fetur ya jefa ‘yan Najeriya da kamfanoni cikin matsin tattalin arziki, musamman saboda karin kudin sufuri da makamashi.
Ya ce gwamnatin Tinubu na kokarin rage wannan matsin ta hanyar karfafa amfani da iskar gas din CNG, wanda gwamnati ta ce zai iya rage kudin makamashi sosai idan aka kwatanta da man fetur.
Onanuga ya ce abin da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne samar da mafita mai dorewa da za ta rage wa ‘yan Najeriya radadin tsadar makamashi, maimakon komawa tsarin tallafin da ya dade yana janyo wa gwamnati matsalolin kudi.
Ya bukaci Atiku da sauran ‘yan siyasa da ke son dawo da tallafin da su bayyana wa ‘yan Najeriya cikakken tsarin da za su bi wajen aiwatar da manufar.
Ya ce ya kamata su bayyana nawa shirin zai ci a shekara, daga ina za a samo kudaden, ko gwamnati za ta sake karbar bashi domin daukar nauyin tallafin, da kuma yadda za a kare tsarin daga almundahana.
“Alkawuran siyasa dole ne su kasance tare da lissafin kudin da zai tabbatar da dorewarsu,” in ji Onanuga.
Ya ce muhawarar kan tsadar rayuwa da manufofin tattalin arziki tana da muhimmanci, amma ya kamata a yi ta ne bisa halin da tattalin arzikin Najeriya yake ciki a yanzu, ba bisa tsarin tattalin arzikin man fetur na baya ba.
