Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta fara wani horo na kwanaki huɗu kan Taimakon Rayuwa na Asali (Basic Life Support – BLS) ga ma’aikatan lafiya daga asibitoci bakwai da ke cikin Abuja, domin ƙarfafa matakan kai ɗauki cikin gaggawa da rage mace-macen da za a iya kauce musu.Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Sakatariyar Lafiya da Muhalli ta FCTA kan harkokin yaɗa labarai, Bola Ajao, ta sanya wa hannu, wadda aka bai wa PUNCH Online a ranar Asabar.
An fara gudanar da horon ne a ɗakin taro na Asibitin Gundumar Asokoro, ƙarƙashin Shirin Kasa na Horar da Ma’aikatan Lafiya kan Taimakon Rayuwa na Asali, wanda Majalisar Lafiya ta Ƙasa ta amince da shi domin aiwatar da shi a faɗin ƙasar.
Ma’aikatan lafiya daga asibitocin Asokoro, Maitama, Wuse, Gwarinpa, Kuje, Kubwa da Nyanya ne ke halartar horon, wanda Ƙungiyar Zuciya ta Amurka (American Heart Association) ta amince da shi.
A cewar sanarwar, FCTA ta himmatu wajen tabbatar da cewa ma’aikatan lafiyarta suna ci gaba da samun ilimin dabarun da duniya ke amfani da su wajen ba da kulawar gaggawa.
Ta kuma bayyana cewa gwamnatin FCT na shirin kafa ƙungiyoyin Code Blue a asibitocin babban birnin, domin tabbatar da cewa marasa lafiyar da ke buƙatar kulawa cikin gaggawa sun samu taimako cikin sauri.
“Manufarmu ita ce mu ci gaba da samun nasarori daga lokacin da babu bugun jini zuwa lokacin da aka farfaɗo da majiyyaci. Idan mutane sun san cewa za su iya samun kulawar gaggawa mai inganci da wuri a asibitocinmu, hakan zai ƙara musu kwarin gwiwa da amincewa da asibitocin gwamnati wajen ɗaukar matakin gaggawa da kula da ‘yan uwansu,” in ji Fasawe.
Ta ce za a faɗaɗa horon BLS zuwa sauran asibitocin FCT nan gaba, tare da samar da kayan aikin yau da kullum da sauran abubuwan da ake buƙata domin ƙarfafa ayyukan ba da agajin gaggawa da kula da marasa lafiya.
Ana sa ran mahalarta horon za su fuskanci jarabawa a ƙarshen shirin, inda za a ba wa waɗanda suka cika ƙa’idar da ake buƙata takardun shaidar kammala horon.
Daraktan Kiwon Lafiya na Asibitin Gundumar Asokoro, Dakta Oluseyi Ashaolu, ya bayyana horon a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma yake da matuƙar muhimmanci.