Gamayyar Manoma Biyar (5) Sun Rasa Rayukansu a Wani Haɗarin Kwale-kwale a Jihar Neja

Wani kwale-kwale a jihar Neja ya kife da aƙalla manoma biyar, maza huɗu da kuma mace ɗaya. Mutanen sun rasu ne bayan da wani kwale-kwale ya kife da su a Kogin Kuɗi, da ke Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja.

Hatsarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar 16/08/2026 a ƙauyen Shaba-Woshi-Kpaya, da ke yankin Edotsu.

Rahotannin sun ce manoman sun rasa rayukansu ne a daidai lokacin da kwale-kwalen ya kife a lokacin da yake ƙoƙarin tsallakewa da su zuwa gonakinsu, kasancewar gonakin suna tsallake Kogin, wanda ya tilasta masu hawa kwale-kwalen. 

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja ce ta tabbatar da faruwar lamarin.

Har wa yau, hukumar ta bayyana sunayen waɗanda suka rasa rayukansu yayin haɗari, waɗanda suka haɗa da: Yahaya Abubakar da Usman Abubakar da Lami Hussaini da Baba Ahmadu da kuma Salihu Aliyu. Hukumar ta ce an gano gawarwakin mutanen biyar tare da yi musu sutura a ranar Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Post a Comment

Previous Post Next Post