Gobarar Daji a Spokane, Washington Ta Kona Gine-Gine 600, Ta Tilasta Wa Mutane 60,000 Tserewa

 Mummunar gobarar daji da ta tashi a yankin Spokane, jihar Washington ta Amurka, ta lalata kimanin gine-gine 600, tare da tilasta wa sama da mutane 60,000 barin gidajensu domin tsira da rayukansu.

gobarar daji

Hukumomi sun ce gobarar ta bazu cikin sauri sakamakon tsananin zafi, iska mai ƙarfi da busassun ciyayi, lamarin da ya sa jami'an kashe gobara ke fuskantar ƙalubale wajen shawo kanta. Gobarar ta ƙone gidaje, kasuwanni da sauran gine-gine, tare da raba dubban mutane da muhallansu.

Jami'an agajin gaggawa sun bayar da umarnin kwashe jama'a daga yankunan da gobarar ke barazana, tare da buɗe matsugunan wucin gadi domin karɓar waɗanda suka tsere daga gidajensu.

Jami'an kashe gobara, tare da taimakon jiragen sama da sauran hukumomin agaji, na ci gaba da ƙoƙarin dakile yaɗuwar gobarar da kare rayuka da dukiyoyi. Sai dai hukumomi sun yi gargaɗin cewa sauyin yanayi da iska mai ƙarfi na iya sa gobarar ta ƙara bazuwa.

Gobarar ta kuma haifar da mummunar gurɓacewar iska a yankin, inda aka gargaɗi yara, tsofaffi da masu fama da cututtukan numfashi da su guji fita waje saboda hayaƙin da ya mamaye sararin samaniya.

Hukumomi sun buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa su bi umarnin kwashe jama'a, su guji shiga wuraren da gobarar ke ci, tare da bibiyar sanarwar hukumomin agajin gaggawa yayin da ake ci gaba da aikin kashe gobarar.

Post a Comment

Previous Post Next Post