ran ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu maza biyu da aka samu da laifin yi wa Isra’ila leƙen asiri, kamar yadda ma’aikatar shari’ar ƙasar ta sanar a ranar Litinin.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Iran ke ƙara yawan aiwatar da hukuncin kisa kan waɗanda ake zargi da leƙen asiri.
Tun bayan fara yaƙin Iran da Isra’ila da kuma Amurka a watan Fabrairu, Tehran ta tsananta zartar da hukuncin kisa, inda aka fi zargin yawancin waɗanda aka yankewa hukuncin da yi wa hukumar leƙen asirin Isra’ila aiki.
Kafar yaɗa labarai ta Mizan, mallakin ma’aikatar shari’ar Iran, ta ce an rataye Omid Behzad da Pouria Safvat da safiyar Litinin bayan an same su da laifin aika wa jami’an Mossad bayanan wuraren soji da cibiyoyin tsaro masu muhimmanci.
Mizan ba ta bayyana lokacin da aka kama mutanen biyu ko lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu ba, amma ta ce an same su da laifin “leƙen asiri da haɗin gwiwa da gwamnatin Sahayoniya.”
Rahoton ya ƙara da cewa mutanen biyu sun taimaka wa hukumomin leƙen asirin Isra’ila wajen cimma manufofinsu ta hanyar ba su bayanai kan cibiyoyin soji da tsaro a lokacin yaƙin.
Yawan hukuncin kisa a Iran ya ƙaru tun bayan fara yaƙin da ya ɓarke a ranar 28 ga Fabrairu sakamakon manyan hare-haren haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Isra’ila, waɗanda suka yi sanadin mutuwar jagoran addinin Iran.
A cewar ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, ciki har da Amnesty International, Iran ce ta biyu a duniya wajen yawan aiwatar da hukuncin kisa bayan China.
Ƙungiyar Iran Human Rights mai hedikwata a Norway da kuma kungiyar Together Against the Death Penalty (ECPM) mai hedikwata a Paris sun ce an kashe aƙalla mutane 1,639 a Iran a shekarar da ta gabata, wanda shi ne mafi yawan adadin da aka samu tun shekarar 1989.
A ranar Talata, Amnesty International ta yi Allah wadai da abin da ta kira “ƙaruwar aiwatar da hukuncin kisa,” bayan Iran ta sanar da rataye wasu maza biyu da aka samu da laifin shiga zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar a lokacin hunturu.