Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirin gwamnatin sa na yin sake fasalin Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), domin mayar da ita hukuma mai ƙwarewa wajen gudanar da harkokin zirga-zirga da tabbatar da tsaron masu amfani da hanyoyi.
Matakin na zuwa ne yayin da gwamnan ya jagoranci aikin tabbatar da bin dokokin zirga-zirga a mahadar Kofar Fanfo, inda ya shafe sama da sa'a guda yana sa ido kan yadda direbobi da sauran masu amfani da hanya ke bin umarnin fitilun zirga-zirga.
A cewar wata sanarwa da darakta janar na yaɗa labarai da hulɗa da Jama'a na giidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar, kwamishinoni da sauran manyan jami'an gwamnati yayin wannan sintiri.
Gwamna Yusuf ya umarci direbobi masu zaman kansu, na haya, masu babura masu ƙafa uku (Adaidaita Sahu) da kuma masu tafiya a ƙasa da su riƙa bin dokokin zirga-zirga tare da mutunta fitilun hanya, yana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta sake fasalin KAROTA tare da ƙarfafa ta domin ta riƙa gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa, ta inganta kula da zirga-zirga, ta tabbatar da aiwatar da dokokin hanya da kuma bunƙasa al'adar bin doka a faɗin jihar.
Gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa na samar da ingantaccen tsarin sufuri mai tsari da aminci ga al'ummar jihar.
Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu masu amfani da hanya ke ci gaba da karya dokokin zirga-zirga tare da yin watsi da sabbin fitilun hanya da aka girka, yana mai cewa bai kamata a bar irin wannan gagarumin aikin da aka kashe kuɗaɗe masu yawa a kansa ya zama abin kallo kawai ba.
Gwamna Yusuf ya yi gargaɗin cewa hukumomin da abin ya shafa su sanya ido sosai kan masu karya dokokin hanya tare da hukunta su domin tabbatar da ana amfani da kayan aikin yadda ya kamata.
