Dan takarar gwamnan Jihar Oyo na jam'iyyar ADC, Taofeek Adegoke, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan wani bidiyo ya nuna yana rabon dafaffiyar masara ga magoya bayansa a gefen hanya kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
A cikin bidiyon, an ga Adegoke yana miƙa wa magoya bayansa masarar da kansa, yayin da suke kiransa da "Mr. Governor" tare da rera taken goyon baya. Wasu daga cikin magoya bayan sun dage sai sun karɓi masarar kai tsaye daga hannunsa, suna mai cewa hakan albarka ce.
Bidiyon ya haifar da martani a kafafen sada zumunta, inda wasu suka yabawa Adegoke bisa nuna tawali'u da kusanci da jama'a. Sai dai wasu sun ce irin wannan mataki tsohuwar dabarar yaƙin neman zaɓe ce da 'yan siyasa ke amfani da ita domin jan hankalin masu kaɗa ƙuri'a.
