Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi wa Malam Usman Aliyu, mijin marigayiya Ummulkhairi, malamar Islamiyyar wadda aka kashe a garin Marabar Jos, kyautar sabon gida domin taimaka masa wajen sake gina rayuwarsa bayan wannan ibtila’i.
Idan ba ku manta ba, an kasheMarigayiya malama Ummulkhairi ne yayin da wasu ɓatagarin matasa suka far mata bisa zarginta da satar yara a Maraban Jos da ke Jihar Kaduna, waɗanda yanzu haka suke a hannun hukuma.
Gwamna Uba Sani ya danƙa takardun sabom gidan ga Malam Usman a lokacin da ya kai masa ziyarar godiya, wanda ya samu rakiyar Sheikh Haliru Maraya.
A baya dai, tun bayan faruwar al'amarin ba jimawa, an hango gwamnan da tawagarsa a lokacin da ya kai ziyara ga iyalan marigayiyar domin jajanta musu, tare da tabbatar musu cewa gwamnatin jihar Kaduna ba za ta tsaya ga iya kalaman ta’aziyya kawai ba.
Baya ga kyautar gida da ya yi ga iyalan marigayi har ya kuma haɗa masu da tallafin kuɗi. Haka nan, gwamnatin jihar ta Kaduna ta ɗauki alƙawarin ɗaukar nauyin karatun ’ya’yan marigayiyar har su kammala karatun, domin jin ƙai da tabbatar da samun kyakkyawar makoma a gare su.
Gwamnan ya bayyana wannan matakin da ya ɗauka a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatinsa na tallafa wa iyalan da suka fuskanci irin wannan mummunan lamari tare da taimaka musu wajen farfaɗo da rayuwarsu.