Gwamnatin APC Ta Haramta Buga Fasfo A Wasu Rassan Jihohi Guda 10, Shida Daga Cikin Duk Daga Arewa

Hukumar Kula da Shigi da Fici ta Ƙasa (Nigeria Immigration Service), da ke da matsuguni a Abuja, ta fitar da wata sabuwar sanarwar hana buga sabon fasfo da wasu takardun tafiye-tafiye a jihohin Arewa guda 6 da kuma wasu jihohin guda 4. 

An fara ganin takardar sanarwar ne a safiyar yau Talata 04/08/2026. Takardar da aka wallafata a ranar Litinin 03/08/2026, wadda take ɗauke da sa hannun mataimakin Kwantirola na ƙasa TO Olaiya, a madadin kwantirolar.

Takardar na ɗauke da saƙon cewa, daga rana irin ta jiya Litinin 03/08/2026 zuwa ranar Litinin 10/08/2026, hukumar ta haramta wa wasu rassanta guda goma buga sabon fasfo da wasu takardun na tafiye-tafiye, tare da ba su umarnin duka waɗannan rassan da su kuma babban reshen buga fasfo na ƙasa zuwa wancan lokacin da aka ɗibar masu wato 10/08/2026. 

Rassan da aka hana buga sabon fasfo ya shafi rassan jihohin Arewa ne guda 6 daga cikin jihohi guda goma da abin ya shafa. Daga cikin rassan akwai: 
1. Reshen Farm Center
2. Reshen Dawakin Kudu
3. Jalingo
4. Gombe
5. Yola
6. Bauchi

Sai kuma sauran huɗun da suka fito daga sassan ƙasar da suka haɗa da: Port Hacourt da Uyo da Calabar da kuma Yenagoa.

Ya zuwa yanzu, da yawan al'ummar Arewa suna kallon wannan a matsayin wani bi ta da ƙulli na siyasa. Wanda suke ganin lallai wannan an ƙara jefa arewacin ƙasar cikin wani mawuyacin hali. Domin yanzu mutum ba zai sami fasfo ba dole sai ya dangana da Abuja ko Lagos,maimakon da da za ka iya samun yi a nan kusa da kai cikin Arewa, kuma cikin kwanciyar hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post