Shugaba Bola Tinubu ya amince da ƙarin albashi da ke tsakanin kashi 30 zuwa 80 na dukkan ma’aikatan sojojin Nijeriya.
Kusan ma’aikata dubu ɗari biyu da hamsin (250,000) ne za su amfana da wannan sabon tsari.
A ƙarƙashin sabon tsarin da zai fara aiki daga ranar 1 ga Satumba, jami’an da suka kai matsayin Laftanal Kanal za su samu ƙarin albashi na kashi 30. Wanda ya shafi masu muƙamin: Janaral Briged daJanaral Meja da Janar Laftanal da kuma Janar.
Ma’aikata daga matsayin Laftanal Kanal har zuwa Warant Ofisa za su samu ƙarin kashi 50, yayin da daga matsayin Kurtu (Private) har zuwa Staff Sergeant za su samu ƙarin kashi 80.
Wannan sabon tsarin albashi, zai mayar da jimillar kuɗin da ake kashewa a shekara kan albashin ma’aikatan sojoji daga Naira Biliyan 660 zuwa Naira Biliyan 924.
Shugaba Tinubu ya kasance yana yaba jajircewa da sadaukarwar da mambobin sojoji ke yi yayin da suke fuskantar barazanar ‘yan fashin daji, garkuwa da mutane da ta’addanci a wasu sassan ƙasar.
“Ya kamata a tallafa wa maza da matan da ke tabbatar da tsaron mu a gidajen mu, a kuma yaba musu a yayin gudanar da ayyukansu na hidima ga ƙasar mu.
“Gwamnatin mu za ta ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin sojoji tare da zamani ta hanyar samar musu da makamai da kayan fasaha da suke buƙata domin gudanar da ayyukansu.
“Gwamnatin mu ta yi imani cewa babu wata ƙasa da za ta iya cim ma babbar nasara ba tare da tsaro ba. Don haka muna da ƙudirin gaske na tattara dukkan dakarun soja da na tsaro domin kawar da barazanar tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan Nijeriya.
“ Ina roƙon sojoji da su ɗauki wannan alheri namu a matsayin alamar godiya mai zurfi kan hidimar da suke wa ƙasarmu. Tare za mu shawo kan maƙiyan da ke son lalata tsarin ƙasarmu.”
Bayo Onanuga
Mataimaki Na Musamman Ga Shugaban Ƙasa
(Bayani da Dabarun Yaɗa Labarai)
4 ga Agusta, 2026