Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Amince da Alawus Na Naira ₦300m

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Kwamitin Tattaunawa mai mambobi tara don ganawa da kuma duba buƙatun Ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) reshen Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), da sauran ƙungiyoyin ma'aikata na jami'ar.

Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Dr. AbdulKadir Mu’azu Meyere ya fitar, ta bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya amince da biyan Naira miliyan 300 a matsayin Alawus ɗin Aikin Koyarwa (Earned Academic Allowance, EAA) a lokaci guda.
Malam Meyere, ya nuna cewa wannan tallafi yana nuna ƙudirin gwamnatin wajen inganta jin daɗin ma'aikata, da kyautata alaƙar aiki da kuma tabbatar da kwanciyar hankali a Jami'ar ta hanyar tattaunawa mai ma'ana da kuma samar da mafita mai ɗorewa.

A cewarsa, tallafin Alawus ɗin Aikin Koyarwa (EAA) na Naira miliyan 300 ya biyo bayan ƙoƙarin da gwamnatin Uba Sani ke ci gaba da yi na biyan bashin sama da Naira miliyan 800 na haƙƙoƙi da alawus-alawus da suka taru tun daga shekarar 2016.

Sanarwar ta lissafa wasu tallafin da gwamnatin Uba Sani ta bayar a cikin shekaru uku da rabi da suka gabata, wanda ya haɗa da biyan basussukan albashin da aka riƙe a baya.

Ban da wannan, gwamnati mai ci ta biya sama da Naira miliyan 300 don tantance shirye-shiryen karatun digiri da kuma aikin duba kayan aikin koyarwa don shirye-shiryen karatun digiri na biyu.

Sakataren Gwamnatin Jihar ya kuma lissafa batun fitar da kuɗaɗe don biyan bashin alawus ɗin duba ɗalibai na SIWES; da kuma kafa tsarin tsayar da Naira miliyan 50 duk wata don tsara yadda za a ci gaba da biyan sauran basussukan da ake bi.

Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan Ilimi, Farfesa Abubakar Sani Sambo ne zai jagoranci Kwamitin Tattaunawar, ya kuma ƙara da cewa Kwamishinab Kasuwanci, Ƙirƙire-ƙirƙire da Fasaha, Malama Patience Fakai; da Kwamishinar Matasa, Malama Gloria Ibrahim suma mambobi ne a cikin kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Shugaban Hukumar Kula da Ma'aikatan Ƙananan Hukumomi, Farfesa Ladan Sharehu da Darakta Janar na Hukumar Tabbatar da Ingancin Makarantu ta Jihar Kaduna, Farfesa Usman Abubakar Zaria da Mataimakin Shugaban Jami'ar KASU, Farfesa Abdullahi Ibrahim Musa da Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami'ar (Pro-Chancellor), Dr. Ibrahim Umar, Babban Sakatare na Sashin Ayyuka na Musamman da ke Ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, shi ma mamba ne, yayin da Babban Sakatare a Sashin Ma'aikata da Horarwa zai yi aiki a matsayin Sakataren kwamitin.

Kwamitin wanda ke da makonni huɗu don kammala aikinsa da kuma gabatar da shawarwari ga Gwamnati, an ba shi alhakin duba bukatun ƙungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da kuma NAAT.

Sanarwar ta ci gaba da cewa kwamitin zai duba Alawus ɗin Haɗaɗɗun Kayan Aikin Karatu (CATA); ya kwatanta yanayin da KASU ke ciki da abubuwan da ake gudanarwa a wasu jami'o'in jihohi; da kuma tantance yawan kuɗaɗen da za a buƙata don aiwatar da buƙatun da suka taso daga yarjejeniyar ASUU da Gwamnatin Tarayya ta shekarar 2025.

Sakataren Gwamnatin ya lura cewa ana sa ran kwamitin zai bayar da shawarwarin hanyoyi masu amfani, na adalci kuma masu ɗorewa a ɓangaren kuɗi don warware matsalolin da ke ƙasa.
Ya yi kira ga dukkan ƙungiyoyin da su rungumi tattaunawa da sasantawa da maslaha maimakon shiga yajin aiki wanda zai iya kawo tsaiko a kalandar karatu kuma ya shafi ɗalibai da iyalansu.

Sanarwar ta sake jaddada cewa ƙofofin gwamnati na tattaunawa suna a buɗe kuma ta tabbatar wa da al'ummar jami'ar ƙudurinta na ƙarfafa KASU da inganta jin daɗin ma'aikata da kuma kiyaye ci gaban ayyukan karatu ba tare da katsewa ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post