Harin Rasha Kan Wata Ma’ajiya Kusa Da Kyiv Ya Kashe Akalla Mutane 27

 Wani hari da Rasha ta kai kan wata ma’ajiya kusa da Kyiv, babban birnin Ukraine, ya kashe aƙalla mutane 27, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Harin Rasha

Rahotanni sun ce harin ya lalata ginin ma’ajiyar tare da jikkata wasu mutane. Jami’an ceto sun shiga aikin neman waɗanda suka makale a ƙarƙashin baraguzan ginin tare da kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci.

Harin ya zo ne yayin da ake ci gaba da gwabza yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, wanda ya jima yana haddasa asarar rayukan fararen hula da lalata ababen more rayuwa.

Hukumomin Ukraine sun yi Allah-wadai da harin tare da kira ga ƙasashen duniya da su ƙara matsa wa Rasha lamba domin dakatar da hare-haren da ake kai wa yankunan fararen hula.

Post a Comment

Previous Post Next Post