Fitaccen mai sharhi kan harkokin jama’a, ɗan jarida kuma marubuci a Kano, Bello Muhammad Sharada, ya rasu yana da shekaru 56.
Sharada ya rasu ne a ranar Asabar a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano , bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Marigayin ya shahara wajen sharhi da nazari kan al’amuran siyasa da sauran batutuwan da suka shafi Najeriya, musamman ta kafafen sada zumunta, ciki har da Facebook.
Bello Sharada ya kasance mai goyon bayar siyasar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau.
A tsawon rayuwarsa, ya taka rawa wajen bunkasa muhawarar jama’a ta hanyar rubuce-rubuce da sharhinsa kan sauye-sauyen siyasa da sauran al’amuran ƙasa.
Bayan rasuwarsa, abokai, abokan aiki da sauran al’umma sun bayyana alhininsu, inda suka bayyana marigayin a matsayin mutum mai kishin rubutu da bayar da gudunmawa wajen wayar da kan jama’a.
An shirya gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:00 na safe ranar Lahadi a Sharada Fegi, cikin ƙaramar hukumar Kano Municipal, bisa tsarin addinin Musulunci.
Marigayin ya rasu ya bar iyalansa da sauran ’yan uwa.
