Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ceto mutane 13 bayan wani gini ya ruguje a yankin Dan Dishe, Kwanar Yashi, da ke Ƙaramar Hukumar Ungoggo ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kano.
A cewar sanarwar, hukumar ta samu kiran neman agaji da misalin ƙarfe 4:32 na asubahin ranar, daga wani jami’in hukumar mai suna Aminu Sani-Warure, da ke aiki a sashen karɓar kiran gaggawa na hukumar.
Sanarwar ta ce, bayan samun rahoton, hukumar ta gaggauta tura jami’an kashe gobara zuwa wurin da lamarin ya faru.
Hukumar ta bayyana cewa har yanzu ana gudanar da bincike domin gano musabbabin rushewar ginin.
Hukumar kashe gobara ta kuma yi kira ga jama’a da su riƙa bin matakan kariya da suka dace, musamman a lokacin damina, domin kauce wa faruwar irin waɗannan hadurra.
