Kungiyar Bayar da Jin Kai ta PLM Ta Raba Kayan Jin Kai Na Buhunan Hatsi 250 Masu Nauyin 20kg Ga 'Yan Gudun Hijira a Rimaye.

Yawan hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a kai a kai, musamman a kan al'ummomin Unguwar Guru, da Hayin Kwanta da Walawa, da Yantari, da Tudun Wulli, da kuma Sukuntuni da sauran ƙauyuka maƙwabta a Gundumar Rimaye sun tilasta wa iyalai da dama tserewa daga gidajensu domin neman tsira.

A yau, yawancin waɗannan mutane da abin ya shafa sun samunl maɓoya ne a wajen danginsu da ke cikin garin Rimaye da sauran garuruwa da suka fi inda suka baro tsaro. Sai dai an bayyana cewa 'yan gudun hijirar na cikin wani matsanancin hali bayan rasa gidajensu da hanyoyin neman abincinsu.

Domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa, tare da rage masu radaɗin abin da ya faru, ƙungiyar Progressive Like Minds (PLM), ƙarƙashin jagorancin Alhaji Tijjani Rabe, ta raba buhunan hatsi guda 250 masu nauyin kilogiram 20 (20kg) ga iyalan da abin ya shafa domin taimaka masu wajen rage musu raɗaɗi.

Yayin da wannan tallafi yake samar da sauƙi na ɗan lokaci, muna addu'ar ganin ƙarshen matsalar 'yan bindiga, dawo da zaman lafiya da tsaro a duk faɗin al'ummominmu, da kuma komawar kowace iyali da ta rasa muhallinta zuwa mahaifarta cikin aminci.

Allah Mai Girma da Ɗaukaka (SWT) Ya kare mutanenmu, Ya samar da zaman lafiya mai dorewa a ƙasarmu, kuma Ya saka wa duk wanda ya ba da gudunmuwa a wannan ƙoƙari na jin ƙai da sakamako mai yawa. Amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post