Lakurawa Sun Kashe Mutane Sama Da 32 A Wani Harin Kisan Kiyashi Da Suka Kai Garin Angushi Da Ke Jihar Sokoto

Ɓarayin dajin da ake kira da Lakurawa, sun kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da talatin da biyu a garin Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto.

Bayanai sun nuna cewa, ɓarayin dajin asun kuma ƙona motoci uku da shaguna biyu da kuma gidaje bakwai, wanda albarkacin ruwan sama ya sa gobarar ba ta yi wata ɓarna ta a zo a gani ba.

Rahotanni sun nuna cewa, mutanen gari da sauran jami'an tsaro sun hallaka 'yan bindigar guda goma sha 13 a yayin doguwar musayar wuta da suka ɗauka suna yi. 

An bayyana cewa, al'amarin ya faru ne, a ranar Juma'a daidai lokacin da al'ummar garin ke cikin masallacin juma'a. Wanda Lakurawan suka shigo wajen ƙarfe 2:15pm a mashinansu da ba a iya ƙayyade yawansu ba. Bayan an fito daga sallar ne suka kashe mutane 5 nan take. Bayan sun tafi kuma suka sake dawowa suka sake kashe wasu mutanen guda biyu a saman wani tsayin. Wanda daga nan ne kuma suka shiga harbin kan mai uwa da wabi. Sai dai wani mai bayar da rahoton lamarin ya bayyana cewa, ya ji ɓarayin suna faɗin a kashe duk namijin da aka yi arba da shi amma ban da mata da kuma ƙananan yara. Lamarin da ya jawo asarar rayuka talatin da biyu (32), yayin da kuma wasu mutanen kuma suka bazama neman 'yan'uwansu.

Ya zuwa yanzu dai, mun sami labarin bayyanar babban kwamandan rundunar sojojin Nijeriya ta 8 (GOC) na rundunar sojin da ke Sokoto zuwa ƙaramar hukumar Kebbe a yammacin ranar Lahadi, domin taya su jaje da kuma yunƙurin kawo ƙarshen ta'addanci a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post