A daidai lokacin da siyasar Najeriya ta fara ɗaukar zafi bayan buɗe ƙofar yaƙin neman zaɓe gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027, shugaban kasar Bola Tinubu ya fitar da jerin sunayen ƴan kwamitin yaƙin sake zaɓensa a zaɓen mai zuwa.
A makon da ya gataba ne a hukumance aka fara yakin neman zabe, kamar yadda jadawalin zaben kasar, wanda hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato INEC ta tsara.Jerin ya nuna cewa shugaban na Najeriya Bola Tinubu shi ne shugaban kwamitin, sannan mataimakinsa Kashim Shettima ne mataimaki na ɗaya, yayin da shugaban jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar Nentawe Yelwadta ke a matsayin mataimaki na biyu.
Daga nan ne kuma aka jero sauran manyan ƴan siyasa da aka ɗora wa alhakin jan ragamar ainahin ayyukan yaƙin neman zaɓen.
Abdul'aziz Yari:
A cikin jerin sunayen da aka fitar a safiyar Asabar, an naɗa tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta Janar (DG) na kwamitin yaƙin neman zaɓen na APC.
Abdul'aziz Abubakar Yari a halin yanzu sanata ne mai wakiltar Zamfara ta arewa a majalisar dattijan Najeriya.
Ya yi gwamnan jihar Zamfara daga shekarar 2011 zuwa 2019 kuma yana ɗaya daga cikin ƴan siyasar da suka ɗauki hankali bayan kafa gwamnatin Bola Tinubu a 2023, musamman a lokacin da ake fafutikar kafa jagorancin majalisar dokokin tarayya.
Waɗanda za su taimaka wa Yari a matsayinsa na darakta janar su ne:
- Godswill Akpabio - (Shugaban Majalisar dattawan Najeriya) - Mataimaki yankin Kudu I
- Sanata Bamidele Opeyemi - Mataimaki yankin Kudu II
- Mai Mala Buni (Gwamnan jihar Yobe) - Mataimaki a yankin Arewa I
- Tajuddeen Abbas (Shugaban majalisar wakilai) - Mataimaki yankin Arewa II
- Barau Jibril - Mataimaki yankin Arewa III.
- Muhimmin wuri a yakin zabe shi ne sakatariya, inda a wajen ne ake shirya yadda kamfe zai wakana, da kuma yadda za a tsara shiga zabe da tsare-tsaren samun nasara.
A wannan karon, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma ke jam'iyyar mai mulki ta naɗa a matsayin sakataren kwamitin yaƙin zaɓen, inda zai yi aiki tare da sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman, wadanda za su kasance mataimakin sakatare da mataimakiyar sakatare.
Haka kuma a kwamitin an tsara wasu fitattun 'yan siyasa da dattawan jam'iyya da suka haɗa da Chief Bisi Akande, Chief Segun Osoba, Sanata Rochas Okorocha, Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Florence Ita Giwa a matsayin wadanda za su ba shugaban kasa kuma shugaban kwamitin, Bola Tinubu shawara kan harkokin yakin zaben.
Sanata Adams Oshiomhole zai jagoranci ɓangaren tattara magoya baya, yayin da Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa zai kasance mataimakin Darakta Janar mai kula da harkokin gudanarwa.